Masu garkuwa sun kashe matashi bayan karɓar kuɗin fansa miliyan N16

’Yan bindiga sun harbe wani matashi mai shekaru 27 har lahira bayan sun karɓ i kuɗin fansar Naira miliyan 16 da babura uku domin sako shi da wasu mutane tara a Jihar Kaduna.

A ranar 16 ga watan Afrilu ’yan bindiga suka kutsa gidaje a uguwar Iya da ke garin Jere inda suka sace mutane tara sannan suka nemi kuɗin fansa Naira miliyan 30.

Wani mazaunin garin mai suna Shuaibu Hussaini ya tabbatar wa wakilinmu a wayar tarho ranar Laraba cewa masu garkuwar sun kashe Abba ne a ranar Asabar.

Shuaibu ya ce masu garkuwar sun harbe Abba ne a lokacin da wanda ke tattaunawa da su ya kai wa shugabansu Naira miliyan 16 da babura uku a wani wuri da suka yi alƙawari.

A cewarsa, bayan ’yan bindigar sun karɓ i kuɗin da baburan ne shugabansu yaɗaure Abba da igiya ya buɗe masa wuta.

“Ɗaya daga cikin waɗanda ’yan bindigar suka sako ya ce shugaban masu garkuwar ya shaida musu cewa sun kashe Abba ne saboda taurin kai da ya yi musu a lokacin da ake tattauna kuɗin fansar.

“Da ’yan uwan waɗanda aka sako suka nemi Abba suka rasa bayan biyan kuɗin fansa ne shugaban masu garkuwar ya ce musu su je suɗauki gawarsa,” in ji shi.

Hussaini ya ce kisan gillan da ka yi wa Abba ta jefaɗaukacin al’ummar Jere cikin damuwa.

Wakilinmu ya so samun ƙarin bayani daga kakakin ’yan sandan jihar Kaduna, ASP Hassan Mansur, amma hakan bai samu ba.