Masu kuɗi sun fi talaka cin dankalin Hausa saboda tsada – Tijjani Abdullahi

Daga IBRAHEEM HAMZA MUHAMMAD

Masu kuɗi sun fi talaka cin dankalin Hausa, don na Turawa sai masu mulki a Babbarn Birnin Tarayya Abuja, saboda tsadarsa da kuma ƙarancinsa a wannan zamani.

Alhaji Tijjani Abdullahi, wanda shine Shugaban Kasuwar masu sayar da kayan marmari na lambu a unguwar rukunin gidajen Zangon Daura da ke Birnin Tarayya Abuja, ne ya shaida wa Wakilin Blueprint Manhaja cewa, farashin dankalin Turawa ya yi tashin Gwauron Zabo daga Naira 4,000 zuwa 8,000 zuwa 16,000, wanda ya sa har masu kuɗi da dama dake Abuja suka guje masa, inda suka koma wa na Hausa wanda shi ma farashinsa ya haura.

Manomin, kuma ɗan kasuwa, ya ce, “shi dankalin Turawa ba a cika cin sa ba, sai an haɗa shi da ƙwai kuma a soya, amma shi gama-gari na Hausawa, za a iya soyawa, gasawa, dafawa da yin dafa-duka, ko ma a ci shi ɗanye, don ya yi maganin yunwa. Shi ya sa wasu ke masa kirari da ‘hana yara kukan yunwa’.”

Ya kuma ƙara da cewa, “ababen da ke kawo ƙaranci da kuma tsadar farashin kayan abinci sun haɗa da rashin tsaro da zafi saboda canjin yanayi da tsadar takin zamani da kuma rashin tallafa wa manoma daga gwamnatoci.

Bugu da ƙari, ya ce, farashin kayan lambun a yanzu su ne kamar haka: tumatir kilo ɗaya noman gida da na zamani Naira 4,000. Tumatir ɗan lambu Naira 15,000 kwandon roba. Ana sayar da kwandon attaruhu ko tattasai Naira 16,000; sabon dankalin Turawa 16,000, tsohon dankalin Turawa 14,000; dankalin Hausa kuma Naira 4,000; sai kuma albasa Naira 4,000.

Tijjani ya ce, suna sarin babban buhun tsohon dankalin Turawa kan Naira 280,000; sabon dankalin Hausa kuma Naira 250,000, shi kuma babban buhun attaruhu Naira 140,000, yayin da babban kwandon tumatir ake sayarwa akan Naira 120,000 da kuma na albasa a kan Naira 60,000.

Haka kuma ya ce, “mun fi son farashin kayan masarufin ya yi ƙasa, don mu fi sayo da sayar da kayan ga kowa, amma idan farashi ya tashi, ba ma iya sayo kaya da yawa, sannan ga tsadar kuɗin dako wanda ba wata riba daga ƙarshe.”

Ya kuma ce, shekara 22 yana kasuwanci a yankin Kado, amma wannan shekarar ce ta fi kowacce tsadar kayan masarufi kuma da rashin kuɗi ko kuma abinnan da ake yi wa laƙabi da ‘ga mari, ga tsinka jaka’.

Manomin ya shawarci gwamnati da masu ruwa da tsaki da mai’aikatar aikin gona da su zage damtse domin samar da hanyoyin wadata jama’ar ƙasa da abinci, don a samu sauƙin farashinsa duk da albarkar faɗin ƙasa da matasa masu aikin gona da lambu bila-adadin da Najeriya ke da su.