Me ke kawo warin gaba

Daga AISHA ASAS

Mai karatu barkanmu da sake kasancewa a shafin kwalliya na jaridar Manhaja, a yau za mu kawo maku wasu daga kayan gyara na mata, sai dai kafin nan zan so mu ɗan tattauna kan dalili ko dalilan da ke sa gaban mace wari.

Gaban mace wuri ne da ke ɗauke da wani nau’i na ƙamshi da ya saɓa wa wanda gangar jiki ke fitarwa. Wannan ƙamshi dai a wurin wasu suna kiran sa da wari wanda ba a son jin sa, wannan dalilin ne ke sa wasu har turare suke sanyawa a gabansu don kawar da wannan ƙamshin marar daɗi a wurin su. Kaɗan ne suka fahimci cewa, wannan launin iska da ke fita bai zama abin ƙyama ba matuƙar dai an yarda da na jiki ma bai da illa. Kamar yadda aka sani, kowanne ɗan adam na da yanayin ƙamshin jikinshi, wanda kare ma da shi ne yake bambanta mutane.

Sai dai wasu dalilai na sa wannan ƙamsahin na gaba yakan gauraya da wasu abubuwa da muke janyowa, to a lokacin ne zai yi sanannen wari da kowa ke ƙyama.

Warin gaban mace na ɗaya daga cikin manyan ababen da ke kawo mata matsala a gidan aure, domin illolin sa masu yawa ne, tun daga yadda zata dasa ƙyamar ta a wurin mijinta, kasancewar ba wanda yake son jin wari a tare abokin mu’amala irin wannan, ga uwa uba ni’imar mace da yake iya yin nasarar kawarwa cikin ɗan ƙanƙanin lokaci.

Warin gaba yana samuwa ta dalilai da dama, kamar rashin tsafta, wadda ta haɗa da riƙon sakainar kashi da abokan tu’ammalin sa, kamar wando. Rashin damuwa da tsaftar kamfai da muke amfani da shi, ko rashin yin amfani da shi a lokutan fita ko tafiya a ƙasa wadda zai sa duk wata ƙwayar cuta da ta samu damar ratsawa tsakanin ƙafafuwanki kaiwa gare shi, hakan zai sa su taru su haddasa ma ki warin gaba.

A wani lokacin wasu kayan mata na zama silar samuwar warin gaba, saboda ababen da aka haɗa su ba masu tsafta ba ne, ko kuma ma kayan haɗin karan kansu na ɗauke da abinda zai iya zama cuta ba ƙarin ni’ima ba.

Yayin da maigida ya kusance ki, bayan kun kammala, wasu matan na da ɗabi’ar gyara kwanciya, su yi barci, har sai sun tashi salla ne za su wanke wurin. Wannan maniyi da ya fito zai samu awanni a wurin, shi ma zai iya zama silar warin gaba, idan aka mayar da shi ɗabi’a.

Rashin damuwa da inda za mu yi tsugunni na daga banɗaki, shi ma zai iya zama hanyar samuwar warin gaba. A taƙaice dai warin gaba samun sa ake yi ta sanadiyyar wasu nau’in ƙwayoyin cuta da ya kamata mu kawar cikin lokaci ko mu hanasu zuwa wurin, jinkirin zai haifar da wannan matsala ta wurin gaba.

Kuma ya kamata mata su san cewa, warin gaba ba halitta ba ce, domin wasu matan kan kafa hujja da cewa, haka aka haife su da shi kamar warin ƙashi, wannan ba gaskiya ba ne, sai dai jimawar sa a jikin mace zai sa ya yi ƙarfin da zai yi wuyar jin magani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *