Me mata suke so a wajen maza?

Daga MAINA YUSUF ALI

Barkanmu da sake haɗuwa a wani makon a filinmu na zamantakewa daga jaridarku mai farin jin ta Blueprint Manhaja. A wannan makon muna tafe da tambayar wai me mata suke so wajen maza? Tambayar nan mai tsauri ce kuma mai daɗi kamar dai maudu’inmu na makon da ya gabata. Wato wai me maza suke so a wajen mata? Inda muke sa ran shi ma na wannan makon za mu yi sukuwa mu yi zamiya mu cimma matsaya kamar makon da ya gabata.

Sai dai ina ganin kamar wannan tambayar ta fi ta wancan makon sauƙin amsawa. Don sanin kanmu ne mata suna suka tara. Don ta ko’ina sukan bambanta a ra’ayoyi da falsafa ta zaman Duniya. Hatta yanayin kwalliya, kitso da gyaran gashi da abubuwa da dama mata sukan banbanta da juna. Amma batun me suke so wajen maza, kusan dukkan kanwar ja ce. Don suna buƙatar abubuwa iri guda. Ba kamar maza ba da suke da mabanbantan zaɓi a kan mata ba. Sai dai kuma su mazan ba kowa Allah yake yi wa baiwar fahimtar ainihin abinda suke so ba. Kaso mai yawa na aurarrakin da ake ganin sun zama zakaran gwajin dafi wajen ƙarko da daɗewa, fahimtar juna ce.

Kuma musamman daga maza. Maza masu dabara su ne suke yin likimo su samo lagon mace. Wato su gano abinda take so, su ribace shi da ita, sai a zauna lafiya. Maza da yawa sun ɗauka mace dukiya kawai take so. Amma kuma ba za mu rasa jin labarin matan da suka guji masu dukiya suka zaɓi talakawa ba. Ko kuma waɗanda suke a gidan talakawa suka fi samun kwanciyar hankali fiye da gidan daula. Ba za a ce ba a son gidan daula ba, amma mata da yawa ba don daular suke zaune da maza ba. In dai namiji ya iya allonsa, sai ka ga ya shawo kanta an zauna lafiya kuma tana binsa sau da ƙafa. Ita a wajen mace, wanda take so, yake kyautata mata shi ta fi yi wa biyayya. Kar na ja ku da nisa, ga wasu abubuwa da mata suka yi tarayya a wajen abubuwan da suke so wajen maza:

  1. Riƙon mana: Mata suna tsananin son namiji mai amana wanda kowanne sirri suka yi da shi ba zai je gun danginsa ko kishiya ko kuma abokai ya fetsar ba. Kuma ko dukiya ta ba shi ba zai yi mata almundahana ba. Sannan ba zai dinga cin amanarta ta hanyar neman matan banza ba.
  2. Madogara: Mace a rayuwarta dole sai ta jingina da wani wanda zai jiɓanci lamurranta. Tun daga haihuwarta takan dogara da iyaye, idan ta yi aure, miji; idan ta tsufa, ‘ya’ya. Ba ƙaramin ƙunci take shiga ba idan mijinta ya yi watsi da lamurranta ya kasa zamar mata tsani ko kafaɗar da za ta jingina da ita ba. Maza za su iya nuna mata tsayuwarsu ta hanyar ɗaukar nauyin al’amuranta da suka shafi kuɗi (idan da hali), ko tsaya mata idan danginsa ko wasu suka so su tozarta ta. Wannan zai sa ta ƙara so da girmama ka.
  3. Gaskiya: Daga ranar da aka ɗaura muku aure, wasu ma tun kafin a ɗaura, mace tana ganinka kamar iyayenta ne. Kuma tana tsammanin ka zamo mai halin dattako kamar su, har ma a rashin yi mata ƙarya da sauran abubuwa. Don haka, maza sai sun yi taka-tsan-tsan. Ko abubuwan da kake ganin gaya mata ƙaryar ya fi gaskiyar alfanu, ya kamata a yi cikin hikima. Daga ranar da ta gane kai maƙaryaci ne, ko kuma kana ɓoye mata gaskiya, to ta daina ƙimanta ka. Kuma ta daina maka biyayya. Mata da yawa sun fi son ɗacin gaskiya a kan zaƙin baki.
  4. Barkwanci: Dukka mata suna son namiji mai raha da barkwanci wanda zai saka su nishaɗi a koyaushe. Hakan yana da matuƙar muhimmanci wajen daɗaɗa mu’amala a cikin zamanku. Ko a samartaka maza masu barkwanci sun fi saurin tafiya da zuciyoyin mata. Sai dai shawararta ga maza, kada su wuce iyaka wajen barkwanci har abin ya salamce ko ya zama abin haushi ga mata. Ko kuma ya jawo raini tsakaninsu.
  5. Basira da hikima: Kamar yadda maza masu barkwanci suke awon gaba da zuciyoyin mata cikin sauƙi, haka ma maza masu hikima da basira. Kusan dukkan jinsin mata suna son irin waɗannan maza. Mata suna tsananin jin daɗin maza masu magana cikin hikima da tsara zance ba tare da wulaƙanci ko tozarci gare su ba. Ko ɓata musu ta yi, sai su yi amfani da hikima don nuna mata kuskurenta. Sai ka ji zama shiru ba rigima. Rashin iya magana na maza da mata yana daga musabbabin mace-macen aure a ƙasar Hausa.
  6. Mutuntawa: Mata suna son mutuntawa daga maza. Musamman a dinga nuna mata ita ce tauraruwa mai muhimmanci. Banda kallon mata ko nuna mata wasu matan sun fi ta. Amma banda yi mata alƙawarin ƙarya na ce mata ita kaɗai ce ba kishiya. Don idan Allah ya aiko maka ƙaddarar ƙaro aure ba za a zauna lafiya ba. Kuma ƙimarka za ta ragu. Idan kuma kana da mata da yawa, kowacce za ka iya yi mata tabbacin tana da muhimmanci a rayuwarka ba tare da ka nuna wata ta fi wata ba. Nuna mata wasu matan na sama da ita a zuciyarka yana sa mata ƙunci da kuma tsananin kishi da tsanar ka a zuciyarta. Don haka Yayana, guji ɗaga mata murya gaban mutane, idan ta yi maka waya, guji katse ta, idan ya kama dole a katse ɗin, ka kira daga baya ko ka ba ta haƙuri.
  7. Addini da mu’amala mai kyau: Mata na son riƙo da addini a wajen namiji. Suna ƙara jin ƙaunarsa tare da ƙara ƙimanta shi da yarda da shi. Don gani za ta yi saninsa zai hana shi cutar da ita ko ha’intarta. Haka kyautata mu’amala da girmamata da magabatanta. Sannan da taya ta wasu abubuwa na gida komai ƙanƙanata yana ruɓanya sonta da ƙimantaka a zuciyarka.
  8. Kwalliya da tsafta: Ba kamar yadda wasu suke ɗauka ba, mata ma suna son tsafta da ado a wajen maza. Maza da dama sun ɗauka yadda suke son mace da tsafta da ado su ba sa buƙatar su yi. Yayana, ka gwada wannan satar amsar ka gani. Matsalar mata da dama suna ganin rashin girmamawa ne idan miji ba shi da tsafta a nemi ya gyara. Haka ma mazan idan an gyara musu, sai su nuna ɓacin rai. Shi ya sa sai dai ta zauna da kai a hakan sai dai ta gaya wa wasu, ko kuma ta haƙura da kai tana mai tsanarka da ganin rashin darajarka a zuciyarta. Kai ne jagwalgwala banɗaki, cin abinci a ɓata waje kamar yaro, ba za ka shafa turare ba ko wanke baki sai za ka fita. Haka za ka zo mata shimfiɗa kana tashi. Haba Yayana!
  9. Sarari: Mata ma kar maza suna buƙatar sarari. Ba kullum mace take so miji ya yi ta liƙe mata ba. Tana buƙatar sararin da za ta ɗan sarara ta yi wasu abubuwa nata na kanta. Ko da danginta ko kuma tare da ƙawaye. Wasu mazan sukan tsunduma cikin kishi idan sun ga matarsu tana yin abubuwa tare da wasu. Amma ka ƙyale ta, tana buƙatar wannan sararin. Ba komai za ta yi tare da kai ba. Kamar yadda kai ma wasu abubuwan za ka iya yi tare da abokanka ko danginka. Nanuƙar juna ma wani lokacin yana sa gundura. Musamman idan saɓani ya shiga, wannan sararin yana da matuƙar muhimmanci don ta yi nazari ta huce ko ta fahimci inda matsalar take.
  10. Abokin Shawara: Mace tana buƙatar namiji abokin shawara. Wanda idan ta zo masa da matsalarta zai ba da lokaci ya saurare ta kuma ya ba ta shawara. Ko da bai ba ta shawarar ba, a wajen mace wannan sauraren nata nuna kulawa ne gare ta. Ba wai ta kawo matsala ka yi ta gwasale ta ba. Hakan yana sa ta kasance cikin ƙunci da kaɗaici. Sannan kuma girmanka zai ragu a idonta.
  11. Kulawa: Dukkan ɗanadam yana buƙatar kulawa. Hadisi ne na Manzon Allah (SAW) Ya bayyana mana ɗabi’ar zuciya guda biyu; Na son mai kyautata mata da ƙin mai ɓata mata. Don haka a dinga ba wa mace kulawa ta hanyar nuna mata soyayya a aikace, kamar ba ta kyaututtuka ko da ba manya ba, yi mata maganganu masu taushi da duk wani abu da zai faranta ranta. Da ba ta tabbacin kana tare da ita duk rintsi.
  12. Imani/Tausayi: Fiye da komai mata sun fi son tausayawa daga namiji. Domin a wajenta tausayi shi ne ƙololuwar son da za ka nuna mata. Kamar damuwa da damuwarta musamman idan tana cikin halin ƙunci kamar mutuwar wani nata ko kuma rashin lafiya da damuwa. Maza masu tausayi kamar gwal suke a wajen mata. Saboda tsadarsu da ƙarancinsu da kuma darajarsu. Duk macen da ta same su, ta rabauta da kadara mai daraja.
  13. Rashin zargi da ƙuntatawa: Mata ba sa son maza masu zargi da son bibiyar duk abinda suke ciki. Wannan yana sa namiji mai halayyar ya fita daga ran mace fit! Kuma kamar yadda na faɗa a baya, a gurin mace, so shi ne girmamawarta. Daga lokacin da ka rasa soyayyarta, ka rasa girmamawar.
  14. Jan aji: Mata suna matuƙar son jan aji. Wajen maza. Duk da wani lokacin za su dinga cewa ba sa so, amma a ƙasan zuciyarsu kana burge su. Kuma suna girmama ka. Don haka, Yayana ba sai an ta zaƙewa gun mace ba. Idan ka ja ajinka sai ka fi ƙima.
  15. Gwarzantaka: Mata suna son mijinsu ya zama gwarzo a dukkan fannin rayuwar aure. Kama daga neman kuɗi don ɗaukar dukkan buƙatunsu ita da yaranta har i zuwa sauran abubuwa.
  16. Adalci: Mata suna matuƙar so maza masu adalci ko da a tsakanin ma’auratan ne ko kuma a tsakanin matansa idan ba ita kaɗai ce ba. Ko ba za ka ce ita ka fi so ba, a ƙalla kada ka nuna mata wata ta fi soyuwa ko ƙima fiye da ita a wajenka. Duk runtsi nuna mata kana sonta tare da ‘ya’yanta.

Saboda haka, nake ce wa maza, ga shawara kyauta kuma satar amsa ta mallakar mace su samu dukkan girmamawar da suke so wajen matansu. Domin girmamawar ita ce burin duk wani magidanci. Haka za ka samu zaman lafiya mai yawa a gidanka ko da kuwa ana auren mata 10. Mace ita ba wayo gare ta ba sosai kamar namiji. Kana ɗabbaƙa wasu ma daga abubuwan da na zana, ka saye zuciyarta. Za ta mallaka maka kanta da duk wani abu da ta mallaka. Kuma za ta bi ka. A nan zan tsaya, sai wani makon za mu haɗu a wani maudu’in, idan rai ya kai.