Me ya sa ƙasar Sin ta dinga yaƙi da cutar COVID-19 har tsawon shekaru uku?

Daga CMG HAUSA

Tambaya:

Tun da galibin mutane za su kamu da cutar COVID-19, me ya sa Sin ta dinga yaki da ita har tsawon shekaru uku?

Amsa:

Hakan ya samar wa al’ummun Sinawa tsawon lokaci na kare kansu.

A cikin shekaru uku da suka gabata, nau’in kwayar cutar COVID-19 yana ta canzawa, wanda hakan ya kawo sabbin kalubaloli ga aikin rigakafin kamuwa da ita bi da bi.

Idan muka waiwayi baya, za mu iya ganin cewa, kasar Sin ta shafe shekaru uku tana aiki tukuru, ta kuma samu “muhimmin lokaci na matakai uku”: lokacin mataki na farko, wato lokaci mafi muhimmanci shi ne, kwayar cutar Delta ta sauya zuwa ta Omicron, yawan gubarta ya ragu sannu a hankali.

Sannan lokacin mataki na biyu shi ne, kasar Sin ta samu lokacin hada-hadar magungunan rigakafin cutar, musamman ma fitar da nau’o’in rigakafi kirar Sin masu yawa.

Kana mataki na uku shi ne, a cikin wadannan shekaru uku da suka gabata, yawancin Sinawa sun karbi allurar rigakafin.

Tun da farko, kasar Sin ta zabi wata hanyar da ta sha bamban da ta kasashen yammacin duniya wajen yaki da cutar.

Lokacin da wani batu ya shafi dubun-dubatar mutane har zuwa mutane fiye da biliyan 1, ana bukatar karfin zuciya a lokacin da ake sa niyya da kuma yin zabe. Wannan niyya ma ta sha bamban da ta kasashen yamma.

A takaice dai, dalilin da ya sa gwamnatin kasar Sin ta yi haka shi ne, ta sanya kare al’ummunta a gaban komai.

Mai fassara: Safiyah Ma