Ministocin harkokin wajen Sin da Jamus sun tattauna ta wayar tarho kan batun yanayin da ake ciki a Ukraine

CRI HAUSA

Mamban majalisar gudanarwar ƙasar Sin, kana ministan harkokin wajen ƙasar Wang Yi, a jiya Asabar, ya tattauna ta wayar tarho da ministar harkokin wajen ƙasar Jamus, Annalena Baerbock, inda suka yi musayar ra’ayoyi game da halin da ake ciki a ƙasar Ukraine.

Wang ya ce, ƙasar Sin tana mayar da hankali matuka game da halin da ake ciki a Ukraine, kuma tana goyon bayan duk wani ƙoƙari mafi dacewa na kashe wutar rikicin, da kuma cimma nasarar warware rikicin ta hanyoyin siyasa.

Game da batun tsaron Turai, Wang ya ce, kamata ya yi a ɗauki damuwar dukkan kasashe da muhimmanci, ya ƙara da cewa, biyo bayan zagaye biyar na aikin ƙara shigar da mambobi cikin ƙungiyar tsaron NATO a gabashin Turai, ya kamata a yi ƙoƙarin daidaita buƙatun Rasha ta fannin tsaron ƙasa ta hanya mafi dacewa.

Ministan harkokin wajen ƙasar Sin ya ci gaba da cewa, yakin cacar baka ya riga ya zo ƙarshe. Ya zama tilas ƙungiyar NATO ta sake la’akari da matsayarta, da hakkokin dake bisa wuyanta, ya ƙara da cewa, kasar Sin ya yi amanna cewa, wajibi ne a yi watsi da dukkan wani tunani na yakin cacar baka da yin fito-na-fito a ƙungiyance. Ƙasar Sin tana goyon bayan ƙungiyar NATO, da ƙungiyar tarayyar Turai, da ƙasar Rasha, da su koma ga teburin tattaunawar sulhu, kuma su yi ƙoƙarin gina wani tsarin tsaron Turai mai adalci, da inganci da ɗorewa, kuma wacce za ta tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali mai ɗorewa a nahiyar Turai.

Wang ya kuma bayyana cewa, ƙasar Sin ba ta goyon bayan warware rikicin ta hanyar sanya takunkumi, kuma tana matuƙar Allah wadai da matakin ra’ayin sanya takunkumi na ɓangare guda, wanda ya ci karo da dokokin ƙasa da ƙasa.

Fassarawa: Ahmad