Ƙungiyar Citizens Unite ta ƙaddamar da sabuwar manhaja don fito da kyawawan manufofin Osinbajo

Daga WAKILINMU

Ƙungiyar Citizens Unite ta ƙaddamar da kamfe na matsin-lamba ga Mataimakin Shugaban Ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo da ya fito takarar neman kujerar shugabancin Najeriya a 2023.

Domin samun damar cimma burin gamsar da al’ummar Najeriya irin nagarta da kyawawan manufofin da Osinbajo ke da su, ƙungiyar ta ƙaddamar da wata sabuwar manhaja da za ta riƙa yi wa mutane rajistar zama ‘ya’yan ƙungiyar a faɗin Najeriya.

A yayin da ta ke jawabi a wajen taron a babban zauren taro na Sheraton dake Ikeja a Legas ranar Asabar, Shugabar Ƙungiyar, Dr. Maryam Shettima ta bayyana cewa a halin yanzu Najeriya ta na tsananin buƙatar ƙwararru masu sanin ya kamata da gogewa da za a aminta wajen damƙa masu harkokin jagorancin ƙasar nan.

Dr. Maryam Shettima

Maryam Shettima ta yi nuni da cewa a iya hange da binciken da ta yi, babu wanda ya fi dacewa da ya jagoranci ƙasar nan a daidai wannan lokaci kamar Mataimakin Shugaban Ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, tana mai cewa wannan dalili ne ya sa za su ci gaba da matsin-lamba ga mataimakin shugaban ƙasar har sai ya amsa wannan kira domin tsayawa takarar kujera lamba ɗaya a 2023.

Ta ce, tana da yaƙinin cewa Osinbajo ne ke da wannan ƙwarewar da ake buƙata a ƙasar nan a halin yanzu, domin sanya Najeriya cikin jerin manyan ƙasashe na duniya ma su tinƙaho da cigaba.

“Ina tuna lokacin da nake aiki a asibitin Fadar Shgaban Ƙasa (State House Clinic) daga 2012 zuwa 2013, a matsayin ƙaramar ma’aikaciyar jinya, na samu damar kusanci da manyan shugabanni a ɓangarori daban-daban na ƙasar nan, amma ban ga mutum mai hazaƙa, tausayi, sauraron jama’a kamar mataimakin Shugaban Ƙasa ba”

“Ba kawai a ce mataimakin shugaban ƙasa Farfesa ba ne, a’a, mutum ne kuma mai tsoron Allah, mai kyawawan manufofi da son cigaban al’umma, tamkar dai yadda muka gani a tsarin Trader Money da kuma ziyararsa ta kwanan nan a Maiduguri ta Jihar Borno” inji ta.

Ta ƙarƙare da cewa, “Bisa waɗannan dalilan ne muke ƙara roƙonsa da ya fito neman wannan kujera ta shugabancin Najeriya a 2023. Saboda mutum ne maras ƙabilanci ko kaɗan,,” a cewar Maryam Shettima.

Ita ma ‘yar gwagwarmaya Violent Anierobi ta bayyana cewa muna da miliyoyin matasa masu son cigaban ƙasar nan, wasu ma suna can a kasashen waje ba su sha’awar dawowa gida saboda halin cin hanci da rashawa da ta dabaibaye Najeriya.

Amma ta ce a wannan karon haƙar matasan za ta cimma ruwa muddin dai Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo ya amsa wannan goron gayyata na tsayawa takarar shugaban ƙasa.

Shi ma a cikin jawabinsa na godiya ga mahalarta taron, Alhaji Alwan Hassan, ya bayyana mataimakin shugaban ƙasa a matsayin mutum na musamman.

Ya ce, “A matsayin malamin makaranta sai da ya kai farfesa, a matsayin lauya, sai da ya kai SAN, a matsayin fasto, sai da ya kai shugaban ɗariƙarsa, sannan a matsayin dan siyasa, sai da ya kai matsayin kujera ta biyu a ƙasar nan. Don haka shi mutum ne na musamman, wanda duk abinda ya runguma, to bil-haƙƙi da gaskiya yake yinsa”, inji Alwan.

Yayin taron ƙaddamarwa

Shi ma fitaccen matsahi McDonald Ehiwe a yayin jawabinsa, ya bayyana cewa akwai tsananin buƙatar matasa su yi taka-tsantsan game ɗaukar matsaya kan wanda za su zaɓa a 2023, domin duk hukuncin da suka yanke zai ci gaba da kasancewa da su na tsawon shekaru takwas ne masu zuwa. Ko dadi ko ukuba.

Taron wanda ya gudana a babban dakin taro na Sheraton dake Legas, ya samu halartar matasa da dama daga dukkan sassar ƙasar nan badan daban