Mun gamsu da jagorancin shugabannin Kasuwar Mile-12 a Legas

Daga DAUDA USMAN a Legas

Wani ɗan kasuwar gwari dake Kasuwar Mile-12 a cikin garin Legas, Alhaji Auwalu na Ubanliba kuma mai bai wa shugaban kulawa da cigaban kasuwanci ɓangaren tumatiri shawara ta musamman, Alhaji Abdulgiyasu Sani Rano, ya bayyana cewar shi da sauran al’ummar kasuwar suna cigaba da gamsuwa tare da amincewa da jagorancin shuwagabanni kasuwar gaba ɗaya.

Alhaji Auwalu na Ubanliba ya yi wannan tsokacin ne a kasuwar Mile-12 a lokacin da yake zantawa da Jaridar Manhaja a Legas dangane da harkokin kasuwancin tumatiri a kasuwar, inda na Ubanliba ya cigaba da cewa haqiqa Abdulgiyasu Sani Rano yana yin iyakar ƙoƙarinsa wajen ganin cewar kasuwar Mile-12 da sauran vangarorinta suna ƙara samun nasarori a wajen kasuwancinsu na yau da kullum.

Hakazalika ya ci gaba da cewa haka shi ma babban shugaban kasuwar ta Mile-12 Intanashinal Market Alhaji Shehu Usman Jibirin Samfam (Dallatun Egbaland) Abeokuta burinsa a kowanne lokaci kasuwar ta ƙara samun bunƙasa da ɗaukaka domin ‘yan kasuwa su cigaba da yin walwala a wajen gudanar da harkokin kasuwancinsu na yau da kullum.

Mai bai wa Abdulgiyasu shawarar ta musamman ya cigaba da zayyano irin ƙoƙarin da shuwagabannin kasuwar suke yi wajen kare mutuncin kasuwar da al’ummar cikinta gaba ɗaya, inda ya ƙara da cewa ko a kwanan nan a wajen gudanar da zaɓubɓukan da suka gabata shuwagabannin kasuwar sun taka rawar gani, domin a cewarsa sun kira taron ‘yan kasuwa kowa da kowa domin wayar masu da kai a game da zaɓen wanda a cewarsa hakan ta sanya aka samu nasarorin kammala zaɓubɓukan cikin ƙoshin lafiya.

Sannan Alhaji Auwalu ya cigaba da jinjina wa Alhaji Abdulgiyasu Sani Rano bisa ga ƙoƙarinsa na tallafa wa marayun kasuwar Mile-12 Intanashinal Market da sauran marasa qarfi da gajiyayyu.