Mun wuce lokacin jiran gwamnati ta ba mu aiki – Aisha Musa

“Akwai sana’o’i da yawa da za mu iya zamanantar da su”

Daga ABUBAKAR M. TAHIR 

A’isha Musa Auyo, matashiya ce wadda take digirinta na uku, kuma mai sana’ar girke-girke, wanda ta zaɓi ta ɗauki wannan ɓangaren domin samun cigaban rayuwarta. Kasancewarta wadda ta yi zurfi a ilimi boko da kuma jajircewarta a neman na kai ta sa Manhaja ta nemi tattaunawa da ita, don jin yadda ta taki wannan matsayi. A sha karatu lafiya:

MANHAJA: Za mu so jin tarihinki a taƙaice.
A’ISHA: Sunana A’isha Musa Auyo, an haife ni ranar 22 ga Fabrairu, 1991. Na yi makarantar firamare da sakandare da kuma makarantar Islamiyya, sannan na yi karantu a Sashen Haddar Alƙur’ani duk a jam’iyar Bayero ta Kano. A lokacin mu kan je makarantar boko da safe, mu je makarantar Islamiyya da yamma. A ranakun ƙarshen mako kuma hadda mu ke zuwa. Na yi digiri na farko a Jami’ar Bayero, Kano, daga shekarar 2008 zuwa 2012, inda na karanci fannin Kimiyyar Halittu masu rai da tsirai wato (Biology Education), bayan na kammala ina jirar zuwa hidimar ƙasa, sai na shiga makarantar koyon girke-kirke da karɓar baƙi, na yi karatun wata shida. Ina kammala makarantar girki na yi aure a shekarar 2012.

Bayan na yi aure, na yi bautar ƙasa, daga 2013 zuwa 2014, sannan na koma ‘degree’ na biyu, inda na karanci ilmin halayyar ɗan Adam ta ɓangaren karatu, wato ‘psychology of Education’. Na kammala ‘masters’ a shekarar 2018, daga nan na ƙara komawa makaranta a 2019 don yin digirin digirgir wato PHD a ‘educational psychology’.wanda na ke kan yi a yanzu haka.

Kasancewar ni ce babba a gidanmu, tun ina ƙarama na ke taya mahaifiyata girki. Na tsinci kaina me matuqar ƙaunar girke-girke. Duk sa’ar da babanmu ya kai mu wurin sayar da kayan tanɗe-tanɗe da maƙulashe a ƙarshen mako, mu na dawowa gida sai na gwada yin abubuwan da mu ka sayo da kaina. wannan ne ta sa mahaifiyata ta kai ni makarantar koyon girki da saukar baƙi bayan na kammala ‘degree’ na na farko.

Yawancin duk sanda mutane suka ci abincina, sukan yi santi, har su ce ya kamata ki buɗe gidan cin abinci. Wannan ta sa na samu ƙaimin fara kasuwancin abinci.

Waɗanne ƙalubale kika fuskanta a sana’ar, ganin cewar ke matashiya ce, kuma ‘yar boko?
To ƙalubale sai dai na ce, alhamdu lillah, gaskiya ba zan iya fidda wani abu guda da zan ce ya zame min ƙalubale ba, sai dai ita dama rayuwa tashi faɗi ce, kuma kowanne abu ya same mu yana koya mana rayuwa ne da yadda za mu fuskance ta.

Wacce shawara za ki iya ba wa mata kan muhimmancin neman ilimi?
Na’am, a gaskiya ina kira ga ‘yan’uwana mata da su daure su yi karatu me zurfi, na boko da addini, saboda mu ne masu yin tarbiyya. Sai mu na da ilimi sosai gudanar da tarbiyya zai ta fi daidai, musamman a wannan zamanin me ruɗu da barazana. Sannan iyaye maza da kuma mazaje, ina roƙonku, ku yi ‘encouraging’ ilimin mata da na yaranku, domin ilmintar da mace ɗaya kamar ilmintar da al’umma ne gabaɗaya. Aure ba ya hana karatu, sannan karatu ba ya hana aure. Sannan ina roƙon ‘yan’uwa da su ta ya mata waɗanda suka haɗa aure da karatu hidimar gida, yadda za su samu su cimma karatunsu. Abu ne na ɗan lokaci. ‘With support’ na miji da ‘yan’uwa insha Allah ba abinda mace ba za ta iya ba. Sannan ke mace mai karatu, ko mai zuwa aiki, ina roƙon ki riqe damar nan da kika samu hannu biyu, ki kama kanki, ki girmama mijinki da kuma al’umma gabaɗaya.

Wacce shawara kike da shi ga matasa da suka kammala karatu mai zurfi?
Shawarata ga matasa waɗanda suka kammala karatu shi ne, su yi amfani da ilmin da wayewar da suka samu a makaranta su gina ma kansu rayuwa mai kyau, wadda su suka tsayama kansu. An wuce lokacin jiran gwamnati ta ba mu aiki. Yanzu akwai ayyuka da sana’o’i da yawa da za mu iya zamanantar da su, waɗanda za su kawo mana rufin asiri da ɗaukaka. Sannan samun sana’ar kai yana da ‘advantage’ na ‘flexibility’ yadda duk inda mutum ya samu kansa, zai iya ɗorawa daga inda ya tsaya. Kamar ni, ina sana’ar girke-girke ‘regardless of my degrees’, na samu kaina me yawo gari daban daban saboda yanayin aikin mai gidana, sana’ar girke-girke nai ta yi duk inda mu ka zauna, saboda ko ina ana buƙatar abinci, sannan ana taro da saukar baƙi.

Haka kuma ina sake kira ga matasanmu, maza da mata da mu tashi tsaye don neman na kanmu, bani-bani ba shi da da daɗi. Sannan ko mu na da mai ba mu, rayuwa ba ta da tabbas, yana da kyau a ce, mu na da wani ‘back up as source of income’. Saboda rayuwa ta yi tsada yanzu.

A’isha musa

Waɗanne nasarori ne za a ce kin cimma a rayuwarki?
Alhamdu lillah, babbar nasara ita ce, samun damar gama makaranta a shekarun ƙuriciya, na kuma fara digirin-digirgir a ƙasa da shekaru talatin. Haka kuma na samu nasarar samun kuɗin shiga, sannan babban abin alfahari na shi ne, ni da ƙanwata Hafsa Auyo, mun koyar da mata fiye da ɗari daga jihohi daban-daban, ‘through online and practical classes’ sana’a wadda za su tsaya da ƙafarsu da kuma yadda za su gyara zamantakewarsu ta hanyar girka ma iyalai abinci mai rai da lafiya da yadda za su sauki baqi. Sannan na samu abin yi mai ɗebe kewa, a duk inda na tsinci kaina, da wuya na tashi ba ni da abin yi, kuma babu abinda ya fi daɗi kamar a ce mutum ya maida abinda ya fi ƙaunar yi sana’arsa.

Wanne kira kike da shi ga ‘yan’uwanki mata kan koyon girke-girke?
Ina kira ga mata da mu daure mu koyi girki na gargajiya da na zamani, saboda girki na taka rawa wajen gyara zamantakewar auratayya, hanyar samun zuciyar namiji shi ne cikinsa. Sannan iyalai za su kasance cikin lafiya saboda abinci mai kyau na ƙara lafiya da annashuwa.

Mun gode.
Ni ma na gode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *