Amfanin zogale ga lafiyar iyali (2)

Daga BILKISU YUSUF ALI

Ci gaba kan amfanin zogale daga makon da ya gabata.

Kamar yadda muka faɗa Zogale yana da matuƙar amfani a jikin ɗan’adam don haka masana kiwon lafiya suke yawan ambatonsa a wurin magance ƙanana da manyan cutoci. Zogale yana da tasiri Allah Subhanahu wata’ala ya yi masa albarka kasancewar bincike –binciken kimiyya sun tabbatar da cewa yana da amfani a fannoni da dama. A kimiyance ana yi wa zogale laƙabi da Moringa oleifera wato Drumstick tree a Turance.

Zogale yana da tasiri kwarai a jiki amma fa yana da ƙa’ida wajen shanya shi ba a son a shanya shi a rana saboda rana tana kashe sinadaransa masu amfani a jiki, sannan kuma saboda ingancin tsafta ana so a shanya shi ne a inuwa ko ma ɗaki cikin ingantacciyar tsafta.

•Garin Busasshen zogale yana magani sosai wajen ba wa hanta kariya sannan ya ba ta abin da take buƙata.

•Yana magance larurorin mafitsara idan aka samu garin zogale wanda aka shanya a inuwa ya bushe aka dake shi aka cuɗe shi da zuma ake shan ƙaramin cokali safe da yamma.

•Zogale yana maganin larurorin fata kamar ƙurajen fuska yamushewar fata da bushewa da sauransu. Ana cin sa bayan an dafa ko kuma a sha ruwansa.

•Garin zogale idan aka haɗa shi da man zaitun mai kyau a cuɗe shi ake shan ƙaramin cokali safe da yamma. Yana magance matsalolin mahaifa kamar fibroid da sauran matsalolin mahaifa wanda sanyi kan janyo.

•Ga wadda ke shayarwa take da ƙarancin ruwan nono ana yin salala na garin Hulba da garin zogale in sha Allah ruwan nono zai wadata kuma za ta samu lafiyar shayarwa sannan ɗan da ake shayarwa zai samu lafiya ingantacciya.

•Ga wanda ke fama da rashin garkuwar jiki a sami ganyen zogale da aka daka da garin tafarnuwa da garin habba a sami zuma mai kyau a gauraya sosai ake shan babban cokali safe da yamma in sha Allah za a samu biyan buƙata.

•Ga macen da take da ƙarancin ni’ima ana samun garin zogale da citta da kanumfari da mazalƙwaila a tafasa su sosai take sha da ɗimi ni’imarta za ta ƙaru.

•Ga wanda ke fama da basur da cushewar ciki in har ya dimanci yawan cin zogale zai zama tarihi.

Amfanin zogale a jikin ɗan’adam ba zai lissafu ba sai dai a tsaya a haka.

Ga mai neman ƙarin bayani ko tambaya kan wani abu day a shafi lafiyar iyali yana iya aiko da tambayarsa ta hanyar wannan lambar 08039475191 ko ta Page dina Bilkisu Yusuf Ali ko a Facebook account ɗina Bilkisu Yusuf Ali.