Gidan aure fagen yaƙi ne!

Daga AMINA YUSUF ALI

Barkan mu da sake haɗuwa a wani sabon mako a shafinmu na zamantakewa na jaridarku mai farin jini ta Blueprint Manhaja. 

Kamar yadda Bahaushe yakan ce, wai ‘aure yaƙin mata’. To a gaskiya aure yaƙi ne na sosai ba ga mata kaɗai ba. A taƙaice ma akwai masanan da suke ganin shi kansa gidan auren ma fagen yaƙi ne. 

Na san masu karatu za su ce fagen yaƙi kuma? Ba wani abu zai kawo wannan tunani ba, sai don ganin shi aure yana samo asali ne daga soyayya. Wacce take wanzuwa tsakanin masoya biyu, kuma so ya zama tubullan ginin sa. 

Yayain da shi kuma  yaƙi kowa ya san yana samo asali ne daga ƙiyayya. Kuma yana wanzuwa tsakanin maƙiyan juna biyu masu burin su ga bayan juna. Amma ina alaƙar aure da ƙiyayya? Ina gamin bahaya da fura? 

Tabbas aure fagen yaƙi ne, amma ba a tsakanin ma’aurata ba. Sai tsakaninsu da wasu maƙiyan aurensu. Kamar yadda na faɗa a baya, yaƙi tsakanin maƙiya biyu ba ya ƙarewa, sai dai a cigaba da fafatawa har guda ya ga bayan ɗaya sannan a ce ya ƙare.

To kuma duk a cikin abubuwa na mu’amalar rayuwa da wahala a samu wanda yake da tarin maƙiya ta ko’ina kamar aure. Kuma dukkan magautan nasa zaƙaƙurai ne sun tanadi makamai masu hatsarin gaske, kuma suna kai masa sara da suka da harbi da ruwan kibbau ta ko’ina. Domin shi abokin gaba babu ta inda ba zai ɓullo maka ba don ya ga ya samu nasarar kai ka ƙasa.

Kamar yadda na sha faɗa a baya, daga ranar da ka ƙuduri niyyar aure, to tamkar ka shata layin daga tsakaninka da magautan aure ne waɗanda dukkansu sun tunkaro ku da zararrun takubba. Amma idan an shirya tsaf da garkuwa, da sulke, da kuma makaman yaƙi masu ƙarko, to za a kai ga nasarar ganin bayan abokan hamayya.

Su waye abokan hamayyar ma’aurata? 

Aure yana da magauta da dama da suka haa da:

  1. Mancewa da mahaliccin auren: Ma’aurata da dama suna manta aure don ibada ake yi ba don shaƙatawa da sauran abubuwa ba. Kuma mun riga mun san cewa, in dai aiki ne na ibada ne, yana tare da sammatsi da taka-tsan-tsan. Sannan akwai shaiɗanu da suke rakaɓe don ganin ya rushe. Don haka dole a durfafi addu’a da tsoron Allah a zaman aure. Kada ku cuci abokan zamanku sai ku ga rayuwa ta yi albarka. Miji ya sauke dukkan haƙƙoƙin mata da ‘ya’yansa dai-dai ƙarfinsa. Haka ma matar ta sauke nauyin da Allah ya ɗora masa nata. Amma fa ba wai kawai tsakanin mata da miji ba. A’a har tsakaninki da kishiyoyi da iyayen miji dukka. Ki zama mai tsoron Allah. Idan an yi haka, to za a samu nasara a kan manyan abokan hamayyar aure wato Shaiɗanu da aljanu. Domin shaiɗanu ko basu samu nasarar kashe aure ba, a ƙalla sukan dage wajen ganin sun lahanta shi ko sun nakasta shi  ba.

Idan kuka yi watsi da dokokin Allah, da addu’o’i sai Allah ya bar ku da iyawarku ku yi ta fafatawa da abokan hamayya, har yaƙi ya ci ku.

  1. Magulmata/mazuga: Magulmata su ma suna daga manyan magautan ma’aurata. Domin magulmata suna da tsananin tasiri wajen yi wa aure kisan mummuƙe wani zubin ma har ya kai shi ƙasa idan mai ƙararren kwana ne. Magulmatan za su iya zama daga dangin ma’aurata, abokai/ƙawaye har ma sauran al’ummar gari da suke da alaƙa ta kusa ko ta neaa da ma’auratan.

Amma fa ma’aurata su sani, gulma da makirci ba sa tasiri sai dai idan da ma can akwai ɓaraka ko rashin yarda ko rashin fahimta tsakanin ma’auratan. Aurarraki sun sha mutuwa a ƙasar Hausa saboda tasirin gulma da makirci. Don haka, kowanne irin labari aka zo wa ma’aurata a kan junansu, su tabbatar sun yi bincike a kai don tabbatarwa. Domin kowanne labari zai iya zama ƙarya ko gaskiya, sai a kiyaye. Wani zubin kuma akan zo wa da mutum da shawara wacce idan ya yi amfani da ita za ta iya rusa masa aure. Miyagun dangi da miyagun abokai sun fi yin haka. Wani ma fa zaman lafiyar da kuke da matarka ba so yake yi ba. Ya fi son kai ma ya gigita naka zaman auren ka zama cikin rashin jin daɗi kamar yadda shi yake.

Sai a dinga duba shawarwari ba kowacce ce ta cancanci a yi amfani da ita ba. Kuma duk matsayin mutum a wajenka, zai iya ba da shawarar da ba za ta dace da kai ba. Domin kai ka san gidanka, kai ka san me ya dace da kai. Wani abin ma idan ka nemi matarka sai ka ga kun warware abinku. Haka ba kowanne sirrin aure ba ne ya cancanci a fitar da shi waje ba. 

  1. Son kai/rashin haxin kai: Kada a ƙyale mutum guda da aiki. Aiki na kowa ne ba mutum guda ba. Kuma kowa da irin rawar da zai taka a ciki. Ya kamata mata da miji su ɗauki kansu a matsayin ‘yan ƙungiyar ƙwallo guda. Waɗanda za su haɗa ƙarfi da ƙarfe domin su cimma nasara. Ba wai ‘yan ɓangarori daban-daban ba. Wannan shi zai sa su haɗa kai da juna su yaƙi ƙungiyar adawa ba wai su yaƙi junanansu ba kamar yadda ma’aurata da dama suke yi a yanzu. Sai ka ga zaman aure ya zama zaman gaba da ƙiyayya tsakanin mace da miji. Sai ka ga miji yana baƙinnciki a kan samun matarsa ko cigabanta da sauransu.

Amma da zai fahimci cewa, ba fa ita ya kamata ya yaƙa ba. Domin a je a zo, da shi da ita dodo guda suke yi wa tsafi. Maƙiyanku na waje ba a cikin gidan suke ba. Domin cigaban juna da samun zaman lafiya a rayuwarku ya ta’allaƙa a kan juna, ko kun fahimci hakan ko ba ku fahimta ba. Ku tuna, ‘yan gari ɗaya ba sa yaƙar juna, sai dai su haɗa ƙarfi su yaƙi abokan hamayya. 

  1. Rashin buɗe ƙofar fahimtar juna: Shi ma yaƙi ne babba da ya tunkaro zaman aurenku. Idan babu fahimtar juna tsakanin ‘yan tawagar yaƙi, akwai matsala. Domin babu ta yadda za a yi a tsara yaƙin yadda ya kamata har a samu galaba kan abokan gaba ba. Wato dai idan muka lura, dukkan dabarar yaqin kare aurenku tana ƙunshe ne cikin fahimtar juna. Sai kun fuskanci juna, kun gano inda zamantakewarku take da rauni sannan za ku magance dukkan wata matsala da za ta iya tunkaro ku. 
  2. Girman kai da rashin amsar gyara: Shi ma wani gingimemen abokin hamayya ne wanda matuƙar kuka bar shi ya yi tasiri, to kuwa zai jijjiga zaman aurenku matuƙa. Idan ba a yi sa ‘a ba ma, ya kayar da shi wanwar ya kwashi ganima. Don haka ma’aurata a rage yi wa juna girman kai. Wasu kuma suna tsoron kada a raina su shi ya sa suke girman kan. Sai ka ga mutum idan ya yi laifi ba zai karɓi laifin ba, sannan ba zai yarda ya yi laifin ba, ballantana a kai ga ya ba da haƙuri ko ta ba da haƙuri a wuce wajen. Amma akwai hanyoyin da mutum zai bi ya samu girman da yake buƙata ba sai ya ƙuntata aboki ko abokiyar rayuwarsa ba. 
  3. Rashin gamsar da juna: Shi ma rashin gansar da juna ta fannin aure abu ne da yake dakushe makaman yaƙinku ya yi wa aurenku ɓarna kaca-kaca. Sai a kula. 
  4. Cin amana: Shi ba alaƙar aure ba, kowacce alaƙa ma yakan ruguza ta. Don haka ma’aurata su riƙe amana. Kada namiji ya fita ya bar mace a gida, ya tafi neman wasu matan. Wallahi Yayana in dai haka ce ɗabi’arka, yaƙi ya nufo aurenka gadan-gadan kuma sai ya murƙushe auren. Haka ke ma mace idan kina da aure kina ha’intar mijinki a al’amuran rayuwa, ko ki dinga neman waninsa, to kin tinkaro yaƙin da ya fi ƙarfinki. Domin ba yadda ma za ki yi nasara a wannan yaƙin. Domin sai ya shigo gidanki ya yi miki rugu-rugu. Ki tafi ba wan ba ƙanin. 
  5. Rashin tajdidin soyayya: Shi kuma rashin tajadidin soyayya shi yake yi wa zaman aurenku kwaf ɗaya ya kai shi ƙas! Ba wani abu tajdidin soyayyar ke nufi ba illa, kulawa da ba wa juna lokaci. tare da sabunta soyayyar junanku da sabunta salon kyautatawarku ga juna duk kuwa da irin daɗewar da kuja yi. Idan ayyukanku suna kwashe ma fi yawan lokacinku, daure ku ƙirƙirar wa juna lokaci domin a dinga ɗan raya soyayyar da iza wutarta kada ta mutu. Sannan idan akwai soyayya mai tsafta ta tsakani da Allah a aure, da wuya yaƙi ya cinye ku. Domin za a samu tausayawa da jinƙai, da fahimtar juna, da girmamawa. Wanda su za su ba ku ƙwarin gwiwar tunkarar kowanne irin yaƙi ne ya fuskanto ku, kuma ku yi nasara. 

Don haka nake kira ga ma’aurata da su zama jarumai a wannan fagen dagar da ake kira gidan aure. Kada su gaza, kuma kada ku guje a fagen yaƙi. Su daure iya wuya su ga abinda zai ture wa buzu naɗi  Domin Jarumi ba ya ƙasa a gwiwa, ba ya tserewa a yaƙi sai ya kai abokan gaba ƙasa sannan ya rusa dukkan shirinsu. 

Idan maatsaloli suka durfafo aurenku, zub da makamai ba naku ba ne. Ku haɗa ƙarfi ku yaƙe su. Domin idan kun guji wannan matsalar yanzu, to gaba sai kun tarar da ita. Domin ba za ku rayu ba aure ba, kuma kowanne gidan aurn kuka sake samu shi ma dai fagen dagar ne, kuma cike da waɗancan magautan. Wataƙila ma su fi na baya jajircewa da son galaba a kanku. 

A nan muka zo ƙarshe, sai Allah ya kai mu wani makon. Masu kiran waya domin yi min tsokaci, ko shawara ko addu’a ko godiya da jinjina, haƙiƙa ni ma ina yin ku sosai. Kuma ni ma ina muku fatan alkhairi. Haƙiƙa ku kuke ƙarfafa mana gwiwa. Na gode sosai.