Matsalar tsaro ba ta hana mu fita aiki ba – Shugaban Direbobin Tanka

Daga MUHAMMADU MUJITABA BIN USMAN

Shugaban ƙungiyar direbobin dakon man fetur na ƙasa, wato ‘Petroleum Tankers Drivers’ (PTD), shiyyar Kano, Katsina, Jigawa da Yobe, Alhaji Sani Malam Garba ya ce kansancewar wannan sana’a ita suka iya Allah kuma ya sa suka dogara da ita, ya ce suna yi wa Ubangiji godiya duk da matsalilin lalacewar hanya da kuma matsalolin tsaro da suka addabi ƙasar, ya ce hakan bai hana su gudanar da aikin su ba.

Sani ya kuma janyo hankalin gwamnati kan gyara hanyoyin ƙasar nan baki ɗaya da kuma shawara kan dakatar da janye tallafin man fetir da gwamnatin ta ci alwashi, wanda ya ce akwai matsala yin hakan, wanda hakan ce ta sa shi cewa ra’ayin su ɗaya da ƙungiyar ‘yan ƙwadago ta NLC kan ɗaukar matakai na yajin aiki bisa doka idan hakan ta kama. 

Shugaban ya kuma nemi jama’a da su yi addu’a kan matsalolin da suka damu ƙasar nan ba a tsaya ana ɗora zargi ga wasu ba.

Haka zalika ya yi amfani da wannan dama wajen jan hankalin al’umma kan matsalolin cunkoso da aka samu a titina sakamakon matocin su da suke tare gurare, inda ya ce wannan ba ya rasa nasaba ko alaƙa da rashin wadataccen gurin ajiye motocin kamar yadda ya kamata. Ya yi kira ga hukumomin gwamnatin Kano kamar su KAROTA da makamatan su na sama musu wajen ajiye motoci da ake ta alwashin samarwa shekara da shekaru a Kano. Ya bayyana cewa su kansu ba sa jin daɗin haka, kuma idan aka ce ba a kawo mai a motocin ba to shi ne ake samun matsalar ƙarancin man fetur.

A ƙarshe Alhaji Sani Malam ya yaba wa gwamanatin Dr. Abdullahi Umar Ganduje kan aikacen-aikacen ta na hanyoyi da gadoji wanda kowa ya ke amfana a Kano da ma ‘yan Nijeriya baki ɗaya.