NAHCON ta ziyarci Hukumar Alhazan Jigawa don shirye-shiryen aikin hajjin 2022

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse

Tawagar Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta ziyarci Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa, domin ganin yadda ta ke gudanar da shirye-shiryenta kan aikin hajji na bana.

Da yake jawabi a lokacin ziyarar, jagoran tawagar kuma babban daraktan duba ayyuka na hukumar aikin hajji ta ƙasa, Alhaji Usman Shamaki ya ce sun ziyarci hukumar alhazai ta jihar Jigawa ne domin duba kayayyakin aikin hukumar dangane da fara shirye-shiryen aikin hajjin na bana.

Ya yaba da irin kayayyakin aiki na zamani da tawagar ta gani a hukumar jin daɗin alhazan ta jihar Jigawa.

A nasa jawabin, muƙaddashin Sakataren zartarwa na hukumar, Alhaji Mustapha Umar ya yaba wa hukumar NAHCON bisa ziyarar gani da ido da suka kawo.

Ya yi nuni da cewar, tuni hukumar ta fara shirye shiryen aikin hajjin bana, yana mai cewar hukumar suna jiran umarni ne daga gwamnatin jihar.

Haka zalika, da yake ƙarin haske, daraktan kuɗi da mulki na hukumar, Alhaji Mustapha Umar da daraktan tsare-tsare, Alhaji Ahmed Umar Labbo da sauran shugabannin sassa sun zagaya da tawagar sassa daban-daban na hukumar domin nuna musu kayayyakin aikin da hukumar take da su ƙunshe a tsarin jadawalin hukumar.