Nan da kwanaki 80 za a kakkaɓe matsalar tsaro a Nijeriya – Ministan Cikin Gida

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola, ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa nan da watan Disamba za a kakkave duk wata matsalar tsaron da ta dabaibaye Nijeriya.

Aregbesola ya bada wannan tabbacin lokacin da ya ke tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN), a Abuja.

Minista ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya bada wa’adin cewa lallai daga nan zuwa Disamba dukkan hukumomin tsaron su tabbatar da sun samar da dawwamammen zaman lafiya a dukkan faɗin ƙasar nan.

Ya ce Buhari ya ce ba zai sauka daga mulki ba tare da ya daƙile matsalar tsaron da ke neman durƙusar da ƙasar nan ba.

“Shugaba Buhari ya bada wa’adin nan da watan Disamba cewa hukumomin tsaro su kakkaɓe duk wata barazanar tsaron da ke addabar rayuka da dukiyoyin ‘yan Nijeriya nan zuwa watan Disamba.

“Na yi amanna cewa dukkan ɓangarorin tsaron qasar nan sun tashi tsaye haiƙan, babu sauran hutu, domin su tabbatar cewa sun kawar da duk wata barazanar tsaro a ƙasar nan.

“Mun maida hankali sosai, da farko misali, sai mu fara tambayar kan mu tukunna, farkon abin da ya wajaba na haƙƙin da ya rataya a wuyan gwamnati, ai shi ne kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

“Saboda haka daga nan zuwa watan Disamba za mu kakkaɓe duk wata matsalar tsaron da ke addabar ƙasar nan.
“Idan ka dubi halin da ake ciki yanzu a Nijeriya, zan iya cewa an samu gagarimin ci gaba a cikin ‘yan shekarun nan,” inji Aregbesola.

Aregbesola ya tunatar da ‘yan Nijeriya cewa kafin 2015 babu inda bama-bamai ba su tashi a Nijeriya.

Yanzu kuma a ta bakin sa, ya yi babu sauran inda ‘yan Nijeriya ke kwana cikin fargaba da tsoron za a dasa masu nakiya a ƙasar nan.

Aregbesola ya danganta fantsamar ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane a sassan ƙasar nan bisa dalilin fatattakar ‘yan ta’adda daga Arewa maso Gabas.

“Kuma mun daƙile masu ɗaukar makamai Kudu maso Gabas, Kudu maso Kudu, Kudu maso Yamma kuma mun daƙile ‘yan ƙungiyar asiri.

“Saboda haka nan da ƙarshen shekara ‘yan Nijeriya za su yi bankwana da matsalar tsaro,” inji Minista Aregbesola.