Nasarar APC a Edo ya tabbatar ‘yan Nijeriya sun yi na’am da salon mulkin Tinubu – Sanata Barau

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Sanata Barau Jibrin ya bayyana cewa nasarar da jam’iyyar APC ta samu a zaɓen Edo nuni ne cewa tabbas ‘yan Nijeriya sun yi na’am da mulkin shugaba Bila Tinubu.

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) bayyana Okpebolo, ɗan takarar jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamna na Edo.

Okpebholo ya samu ƙuri’u 291,667 inda ya doke abokin hamayyarsa kuma ɗan takarar jam’iyyar PDP, Asue Ighodalo, da ya samu ƙuri’u 247,274.

Dan takarar jam’iyyar Labour Party (LP), Olumude Akpata, ya zo na uku da ƙuri’u 22,763, yayin da sauran ‘yan takara 14 suka samu ƙuri’u 8,945.

“Wannan nasara alama ce ta yin na’am salon mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu. “Ina taya zaɓaɓɓen gwamnanmu Sanata Monday Okpebolo murna kan wannan nasara da ya samu.”

Jibrin ya ƙara da cewa shugabancin Abdullahi Ganduje a matsayinsa na shugaban jam’iyyar na ƙasa ya ƙara wa jam’iyyar APC, farin jini, ƙarfi da haɗin kai tare da jagorantar ta har ta kai ga lashe zaɓen Edo.

By ukarofi