Daga GARBA SHU’AIBU DAKATA
Yaƙi da cin hanci shi ne babban kudirin da shugabannin ƙasar Sin suka sa a gaba, musamman bayan babban taro karo na 18 na wakilan jam’iyyar kwaminis mai mulki a ƙasar da aka gudanar a shekarar 2012, inda suka zage dantse wajen yaƙi da cin hanci a bisa doron halaccin tsarin siyasa.
Gwamanti mai ci a yanzu ƙarƙashin jagorancin shugaba Xi Jinping duk da irin ƙalubalen da take fuskanta ta sami gagarumar nasara wajen fito da sabuwar dokar ɗaukar hukunci mai tsanani ga duk wata harkar cin hanci da karɓar rashawa a ƙasar.
A yunƙurin kawo karshen cin hanci a ƙasar Sin, gwamnatin ƙasar ta yi nazari na tsanaki domin gano dalilai da kuma illar da cin hanci da rashawa suka yiwa ƙasar.
Irin matakin da ƙasar Sin ta dauka na kawo ƙarshen cin hanci sun haɗa da kafa hukumomin yaki da cin hanci da rashawa tare da yin hukunci mai tsanani ga duk wanda aka samu da aikata laifin cin hanci.
Haƙiƙa a wannan mataki kwalliya ta biya kuɗin sabulu domin gwamnati da jam’iyyar Kwaminisanci mai mulki sun haɗa ƙarfi wuri guda wajen yaƙar cin hanci da kuma wanzar da hukunci kan doron shari’a ta yadda aka sami tsabtatacciyar gwamnati wadda babu bara gurbi a cikinta.
Irin matakan da gwamnatin ta Xi Jinping ta dauka da zummar cika burinta na kakkaɓe rashawa su ne kafa babban kwamitin binciko laifin cin rashawa na ƙasar.
Wannan kwamiti na binciko laifin cin rashawa ya zamanto kan gaba wajen gano ayyukan rashawa a ƙasar, inda ya binciko laifukan cin hanci da rashawa da kuma hukunta wadanda ke da hannu a ciki sama da mutane miliyan hudu a kowane matakin muƙami na gwamnati. Abin sha’awa a nan shi ne wannan kwamiti na binciko aikita laifin rashawa yana gabatar da wani shiri na ƙashin kansa mai suna “ba gudu babu ja baya wajen kauda rashawa” wato “zero tolerance” a Turance.
Manufar wannan shiri ita ce nuna wa ’yan ƙasa irin nasarar da kwamitin yake samu na yaƙi da karɓar shawara tare da fallasa duk wani hamshaƙin gwamnati da aka samu da aikata laifin cin rashawa komai girman mukaminsa.
A rahoton kwamitin na shekarar 2018 zuwa ta 2020, kwamitin ya bayyana cewa ya yi nasarar kamo ’yan ƙasar da suka tsere zuwa ƙasashen ƙetare kimanin 3848, haka kuma an sami nasarar dawo da kusan biliyan goma na kuɗin ƙasar da aka yi awon gaba da su.
A hannu guda hukumar ta ɗauki matakan kau da cin hanci a ƙasar ta hanyoyi da dama, kaɗan daga ciki su ne, na ɗaya, gwamantin ƙasar Sin ta bijiro da shirin ilmantar da ma’aikatan gwamnati kan riƙon amana da kishin ƙasa ta yadda cin hanci da rashawa ba zai sami gurbi a cikin aikin gwamnati ba.
A dai wannan gaɓar gwamnatin ta tsara jadawalin ilimi a manhajar manyan makarantu na jami’o’i, makarantun sakandare da kuma makarantun firamare.
Duk waɗannan matakai an ɗauke su ne da zimmar fahimtar da ‘yan ƙasa illar cin hanci da rashawa da kuma yadda suke rugurguza manufofin gwamnati na kyautata rayuwar ‘yan kasa.
Babu shakka irin wannan matakai da ƙasar Sin ta dauka sun taimaka ƙwarai da gaske wajen manufofin gwamnati na samar da rayuwa mai inganci ga ‘yan kasa. Abin alfahari ga ƙasar ta Sin a yau shi ne yadda kasar ta yi bikin fidda miliyoyin ‘ya’yanta daga kangin talauci da fatara gami da kuma inganta rayuwar mazauna yankunan karkara, inda aka samar musu mazauni na zamani mai dauke da kayan alatu na more rayuwa kamar a manyan birane na ƙasar ta Sin.
A ƙarshe wannan mataki na kauda cin hanci da rashawa da gwamnatin ƙasar Sin ta dauka karkashin jagorancin shugaba Xi Jinping ya jawowa ƙasar ta Sin kima a idon sauran ƙasashen duniya, haka kuma irin ci gaban da kasar ta Sin ta samu a ɓangaren kimiyya da fasahar zamani ta zamanto gagara gasa a fagen ƙere-ƙere a duk faɗin duniya.
