Sin ta daɗe tana taimaka wa Afirka wajen samun cigaba mai ɗorewa

Spread the love

Daga CMG HAUSA

Ƙwararrun ƙasar Kenya, sun fitar da wani rahoto a kwanan nan, wanda ya bayyana cewa, binciken jin ra’ayoyin jama’a ya nuna cewa, ƙasar Sin ta fi ƙungiyar tarayyar Turai wato EU sauri da aminci, wajen inganta muhimman ababen more rayuwar al’umma a ƙasashen Afirka.

Da yake amsa tambayar da aka yi masa game da hakan, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Sin Wang Wenbin, ya ce tun bayan kafa dandalin FOCAC na tattauna haɗin-kan Sin da Afirka, kamfanonin ƙasar Sin sun shimfida layukan dogo da tsawonsu ya zarce kilomita dubu 10, da hanyoyin mota masu tsawon kilomita kusan dubu 100, tare da gina daruruwan gadoji, da tashoshin jiragen ruwa, da asibitoci, da makarantu da yawa a dukkanin sassan nahiyar Afirka.

Sai dai duk da hakan, wasu mutane na shafawa hadin-gwiwar Sin da Afirka bakin fenti, inda suke ƙoƙarin yayata wani ra’ayi dake ganin baiken ”gina muhimman ababen more rayuwar al’umma masu ingancin gaske”. Sai dai a cewar Wang, mene ne ainihin ababen more rayuwa masu ingancin gaske?

Kuma wanene ke iya ƙoƙari wajen samar da alheri ga al’ummun ƙasashen Afirka? Wadannan tambayoyi ne da su al’ummun Afirka kaɗai za su iya ba da amsar su.

Wang ya jaddada cewa, ƙasar Sin na ganin cewa, ya dace Afirka ta zama wani babban dandamali, na hadin-gwiwar ƙasa da ƙasa, kuma ya kamata ƙasa da ƙasa su ƙara samar da alfanu ga al’ummun Afirka, bisa tushen girmama ‘yancin kansu, da sauraron muryoyinsu.

Fassarawar Murtala Zhang

By Editor