NDLEA ta kama ƙasurgumin mai safarar ƙwayar Tiramol a Nijeriya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar NDLEA ta kama ƙasurgumin ɗan harƙalla kuma mai safarar ƙwayar Tiramol a Nijeriya.

Kakakin hukumar Femi Babafemi ya bayyana a wata sanarwar cewa hukumar ta kama Ugochukwu Chukwukadibia shugaban kamfanin motocin na Autonation Motors Ltd, da rumbun damin ƙwayar tiramol da kuɗin sa ya kai Naira biliyan 8.8.

”An kama ƙwayoyin tiramol sama da miliyan 13 danƙare a gidan Ugochukwu, wani ƙasurgumin attajiri da ke zama a Lekki, Jihar Legas, da kuɗin su suka kai Naira biliya. 8.8.

Wannan kamu da EFCC suka yi ya zo kwanaki kaɗan bayan hukumar ta cafke wani ƙasurgumin ɗan harƙallar ƙwayoyi da shi kusan masana’anta ce a ya ke da ita sukutum na sarrafa ƙwayoyin daban-daban a cikin gidansa, da kuma wata katafaren shagon siyar da magani.

Bincike da aka gudanar kafin a damƙe Ugochukwu ya nuna yana da danƙara-danƙaran gidaje masu a VGC dake Legas, kuma a cikin ɗaya ne yake buga harƙallar ƙwayoyinsa na tramol.

Shugaban hukumar Janar Buba Marwa mai murabus, ya jinjina wa ƙwazon jami’an hukumar bisa wannan babban kamu da suka yi.

Idan ba a manta ba, a cikin makon jiya hukumar ta damƙe wasu mashahuran masu safarar hodar ibilis na ƙasa da ƙasa a Jihar Legas.

Bayan tantance ƙwayoyin da aka kama, hukumar ta ƙona su kaf ɗin su da aka yi musu kuɗi Naira biliyan 198.