NRC ta dakatar da jami’anta 3 kan sakaci da aiki

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Sufurin Jiragen Ƙasa ta Ƙasa (NRC), ta dakatar da wasu jami’anta dangane da gocewar qafar jirgin da ya auku a yankin Kubwa na Abuja kwanan nan.

Gocewar kta haifar da tsaiko ga aikin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna na ɗan lokaci kafin komawa da aiki bayan kwana, kuma bayan kammala aiki a matsalar da ta haifar da gocewar.

Majiyarmu ta ce tuni hukumar ta dakatar da wasu jami’an da lamarin ya shafa sakamakon abin da ya faru wanda a cewar hukumar, sakacin jami’an ne ya haifar da akasin.

Wata majiya ta ce jami’an da ke bakin aiki a ranar da lamarin ya auku sun kasa jan hankalin direban jirgin duk da sun cewa yana gudun wuce misali.

“Ba su zuwa aiki, kuma kwamitin minista kan sufuri zai bincike su kan samun su da laifin da suka aikata,” in ji sanarwa.

By Editor