PDP ta maye gurbin Gwamna Umahi da Igariwey

Daga BASHIR ISAH

Biyo bayan hukuncin tsige gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi da mataimakinsa Dr Eric Kelechi Igwe da Babbar Kotun Abuja ta yi a jiya Talata, jam’iyyar PDP ta bayyana sunayen Hon. Iduma Igariwey da Fred Udeogu don maye gurbinsu.

Shugaban PDP na ƙasa, Sanata Dr Iyorchia Ayu, ya ce jam’iyyar ta miƙa sunayen waɗanda ta zaɓo ɗin ne don maye gurbin tsigaggun ga Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC).

Ayu ya bayyana hakan ne ga manema labarai ran Talata a Abuja.

Kotu ta tsige Gwamna David Umahi tare da mataimakinsa, Dr Eric Kelechi Igwe bisa dalilin sauya sheƙa da suka yi inda suka bar jam’iyyarsu ta asali PDP zuwa APC.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *