
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Wani rikici da ya ɓarke tsakanin ƴan bindiga a ƙauyen Kawaye da ke ƙaramar hukumar Anka a jihar Zamfara ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 30 tare da jikkata wasu da dama.
Hakan ya auku ne sakamakon wasu dabbobi da aka sace.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ɗaya ne daga cikin da yawa da ƴan bindigar ke yi a tsakaninsu wanda hakan ya yi sanadin salwantar rayuka da dama.
Wannan hamayyar da ke tsakanin ɓangarorin ƴan bindigar ya haifar da mace-macce acikin su da ma shugabanninsu wanda hakan ya zama barazana ga zaman lafiyar yankin.
Hakan nan, faruwar al’amarin ya sanya ƙauyukan dake yankin cikin zaman ɗar-ɗar duk da hakan kuma alama ce da ke nuna ƙarfinsu ya fara raguwa ya a shiyyar.
Mazauna yankunan sun bayyana hakan a matsayin dalilin da zai kawo ƙarshe ga ayyukan ƴan ta’adda a yankin.
Kawo yanzu dai babu wani saƙo game da lamarin daga hukumomi yayin da su ke cigaba da kula da halin da yankin ke ciki.
