Rikicin makiyaya da manoma ya yi sanadin ƙonewar gidaje 15 a Guri

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse

Rikici tsakanin makiyaya da manoma a ƙauyen Sakasza dake cikin yankin Ƙaramar Hukumar Guri a Jihar Jigawa ya yi sanadin ƙonewar gidaje 15 daga ɓangarori biyu na abokan faɗar.

Rikichin ya faru ne sakamakon ta’adi da Fulanin suka yi wa manoma a gonakinsu a cikin makon da ya gabata, inda Fulani makiyaya suka sanya shanu a gonakin manoman da tsakiyar rana suka cinye masu amfanin gona.

Hakan ya sa manoman na ƙauyen Sakasza suka ɗauki makamai suka yi wa rugagen Fulanin na Sakasza tsinke suka ƙone masu bukkokinsu suka fatattaki Fulanin daga rigagensu.

Sakamakon haka ne su ma Fulanin suka kai wani samame da tsakiyar daren Asabar suka ƙone gidajen manoma shida a ƙauyen na Sakasza. Lamarin da ya sa aka samu hasarar dukiya mai tarin yawa.

Da yake magana da manema labarai, Shugaban Ƙungiyar Fulani Makiyaya ta Kautal Hore, Malam Kabir Umar Dubantu, ya ce yawun makiya ya nuna takaicinsa akan yadda al’amarin ya faru, saboda a tsakanin manoman da makiyayan akwai zaman lafiya da ƙaunar juna, ya ce bai yi zaton haka za ta iya faruwa ba.

Ya kuma ja kunnen makiyaya ‘yan uwansa da su guji tayar da zaune-tsaye kasancewar su Fulani kamar yadda bincike daga hukumomin ya nuna sune suka fara taƙalar manoman suka sanya masu shanu a gonakinsu, ya ce hakan ba daidai ba ne.

Shi ma da yake tabbatar da fa ruwar lamarin, Kakakin rundunar ‘yan sanda na Jihar Jigawa Lawan Shisu Adam ya ce rikicin ya faru ne tun a ranar Juma’a har zuwa ranar Asabar ta makon jiya, amma ‘yan sanda sun shawo kan rikicin.

Ya ce har zuwa lokacin da muke rubuta labarin babu wanda ‘yan sanda suka kama daga dukkan ɓangarorin biyu kuma suna nan suna ci gaba da bincike domin gano waɗanda suke da hannu dumu-dumu domin a yi masu hukuncin da ya dace da su.

Shugaban ƙungiyar ta Kautal Hore, Malam Umar Kabir ya tabbatar da cewar an ji harbe-harbe a rugagen Fulanin kuma an kore masu shanayensu, lamarin da ya sa aka samu wasu daga cikin Fulanin suka mayar da martani suka yi ƙoƙarin ɗaukar fansa suka ƙone gidaje shida na manoman.