Rikicin Masarauta-Rundunar Ƴan sandan Kano ta kori masu gadi a fadojin da Sunusi da Aminu suke tare da ƙara jami’ai

Daga Farouk Abbas

Rundunar Ƴan sandan Jihar Kano ta aika da ƙarin jami’anta zuwa fadojin da Sarki Sunusi Lamido Sunusi da kuma Sarki Aminu Ado Bayero su ke, biyo bayan ɗar-ɗar na faruwar rikici a yankunan Masarautun.

Tuni dai mafarauta da sauran masu gadin Masarautun suka bar fadojin a lokacin da jami’an suka isa, don inganta tsaro ga rayuka da dokiyoyin al’ummar yankunan.

Kwamishinan Ƴan sandan Jihar, Usiani Gumel ya tabbatar da haka yayin ganawa da manema labarai inda ya ce sun ɗauki matakin ne domin tabbatar da wadataccen tsaro a faɗin Jihar.

Usaini Gumel ya ce “an tura jami’ai a Fadar Ƙofar Kudu inda nan ne Sarki Sunusi yake sannan kuma an tura wasu jami’an zuwa ƙaramar fadar Nasarawa inda Sarki Aminu Ado yake” inji shi.

Gumel ya kuma ƙara jaddada wa al’umma Jihar cewa suna cigaba da ƙoƙarin ganin an samar da isasshen tsaro ga rayuka da dokiyoyinsu, don haka ya yi kira gare su da su taimaka wa hukumar wajen aika musu da bayanai da suka shafi tsaro domin wanzar da zaman lafiya da cigaba gami da samar da ingantacciyar harkar siyasa a faɗin Jihar.

Leave a Reply