A jiya Alhamis, dakarun Faransa suka fara janyewa daga Jamhuriyar Nijar, kamar dai yadda shugaba Emmanuel Macron ya alƙawarta a ranar 24 ga watan Satumbar da ya gabata.
Sojojin Faransa na farko da suka fara ficewa a jiyan su ne dakaru 400 da ke a yankin Walam, daf da iyakar Nijar da Mali, kuma sun kasance suna aikin samar da tsaro ne ƙarƙashin wani shiri da aka yi wa take ‘Operation Almahaou’, wanda babbar manufarsa ita ce samar da tsaro a yankin Liptako.
Waɗannan dakaru za su isa birnin Yamai ne ta ƙasa, amma hakan na buƙatar cikakken tsari da kuma tsaro ga ayarin sojojin daga inda za su tashi har zuwa cikin birnin Yamai.
Duk da cewa tazarar ba ta wuce kilomita cari ɗaya ba, amma dakarun za su iya share tsawon yini biyu saboda rashin kyawun hanya.
Da zarar sun isa Yamai kuwa, nan take dakarun 400 za su fara tashi zuwa Faransa ta jirgin sama.
Rundunar sojojin Faransa dai ta ce, tana fatan gudanar da wannan aiki ne da haɗin-gwiwar mahukuntan Nijar, yayin da sojoji da suka ƙwaci mulki a ƙasar ke cewa ga alama Faransa ba ta da niyyar janye dakarunta daga ƙasar.
Wannan dai gagarumin aiki ne da ya tanadi kwashe sojoji fiye da dubu ɗaya da kuma manyan sunduƙai makare da kayan aikinsu, kuma dole sai an yi amfani da hanyoyi na ƙasa domin jigilar waɗannan kaya a cikin watanni uku.
To sai dai yayin da ake hasashen cewa za a isar da kayan ne a tashar jiragen ruwan birnin Cotonou, tuni mahukuntan sojin Nijar suka ce ba za su buɗe iyakar ƙasar ta ɓangaren jamhuriyar Benin ba.
