’Yan wasan Al-Ittihad sun ƙi buga wasa saboda ajiye mutum-mutumi a ƙofar filin wasa

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

An ɗage wasan ƙwallon ƙafar da aka shirya bugawa a ranar Litinin tsakanin ƙungiyoyin Saudiyya da Iran a gasar cin Kofin Zakarun Nahiyar Asiya, sakamakon ajiye mutum-mutumin tsohon babban kwamanda a rundunar sojin ƙasar Iran Manjo Janar Qassem Soleimani a ƙofar filin da za a fafata wasan.

Har zuwa wannan lokacin dai ba a sanya lokacin da za a kara tsakanin ƙungiyar Al Ittihad ta Saudiyya da Sepahan ta Iran ba, bayan da tawagar ’yan wasan Saudiya ta ƙi shiga filin da ke birnin Isfahan, saboda mutum-mutumin na marigayi Solaimani da aka ajiye a ƙofar shiga cikinsa.

Manjo Janar Soleimani dai ya taka muhimmiyar rawa wajen jagorantar ayyukan sojin Iran a Gabas ta Tsakiya tsawon shekaru da dama, kafin Amurka ta halaka shi a wani hari da ta kai masa a watan Janairun shekarar 2020.

Wannan sabani ya zo ne wata guda bayan da Saudiya da Iran suka ƙulla yarjejeniyar maido da wasannin ƙwallon ƙafa na gida da waje a tsakanin ƙungiyoyinsu, bayan da aka shafe shekaru bakwai ɓangarorin biyu ba sa ziyartar juna, sai dai su fafata a wata ƙasar.

Ƙungiyar Cristiano Ronaldo ta Al Nassr ce ta fara buga wasa a Iran cikin gasar Zakarun ta nahiyar Asiya a ranar 19 ga watan Satumban da ya gabata, wanda kuma shi ne karo na farko da wata ƙungiyar ƙwallon ƙafa daga Saudiya ta shiga Iran tun shekarar 2016.

By Editor