Nijeriya ta shirya ƙarfafa ƙawance da EU don yaƙi da matsalolin tsaro

Spread the love

Ministan Tsaro Mohammed Badaru, ya bayyana cewa a shirye Nijeriya take ta ƙarfafa ƙawance da Ƙungiyar Ƙasashen Turai (EU) a fannin tsaro.

Badaru ya bayyana haka ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin tawagar ƙungiyar a ofishinsa da ke Abuja.

Ya ce “Nijeriya na so ta farfaɗo da ƙawancenta da EU da ƙarfafa dangantaka wajen yaƙi da matsalolin tsaro.

Ya ce lallai Nijeriya na da buƙatar samun kayayyakin aikin tsaro daga ƙungiyar EU don yaƙi da ƙalubalen tsaro a ƙasar.

A cewarsa, “Manyan matsalolin tsaron da Nijeriya ke fuskanta su ne fashin fadaji a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya, sai matsalar Boko Haram a Arewa maso Gabas da satar mai a Kudu maso Kudu, da kuma matsalar masu neman ɓallewa a Kudu maso Gabas da matsalar tsaro a yankin tabkin Chadi.”

Jagorar tawagar kuma Mataimakiyar Babban Sakataren EEAS, Helena Konig, ta ce sun yi ziyarar ne domin sanin inda EU za ta shigo don tallafa wa Nijeriya a ɓangaren tsaro.

By Editor