Mu masu cutar sanƙarar mama muna buƙatar taimakon gaggawa
DAGA MUKHTAR YAKUBU
A ‘yan kwanakin nan ne tsohuwar jaruma a Kannywood Halisa Muhammad ta kafa wata sabuwar ƙungiya ta wayar da kan mata a kan sanƙarar mama wadda a yanzu tuni ta yi nisa da wayar da kan mata tare da samar musu gudunmawa a kan yadda masu larurar za su ci gaba da gudanar da rayuwarsu a cikin yanayin da suka samun kansu.
Halisa Muhammad wadda a yanzu ma take kan shan magani tare da samun kulawar likita domin ceto rayuwarta daga larurar sanƙarar mama ta yi wa wakilinmu a Kano, Mukhtar Yakubu bayani a kan manufa da kuma dalilin ta na samar da ƙungiyar. A sha karatu lafiya.
MANHAJA: Mu fara da jin kowacce Halisa Muhammad, da kuma maƙazudin kafa ƙungiyar wayar da kan mata masu lalaurar sanƙarar mama?
HALISA: To kamar dai yadda aka sanni, ni ‘yan Kannywood ce sama da shekaru 26 , don zan iya cewa da mu aka kafa Kannywood ɗin. Kuma mace ce ni wadda na yi aure sau biyu, ina da yara Alhamdulillah, kuma har yanzu ana cikin gwagwarmayar rayuwa kala kala, kuma ni ‘yar kasuwa ce. Kuma mafsrin samar da ƙungiyar wayar da kai ta masu ciwon sanƙarar mama, ta samo asali ne daga ciwo ne da ni na fuskanta , na shiga cikin larura ta ciwon sanƙarar mama, kuma na samu ilimi a kan abubuwan da suke cikin ta. Don haka sai na ga a matsayina na tsohuwar jaruma ya kamata na yi yekuwar wayar da kai a kan sanƙarar mama, don murya ta za ta je wajen da ta wasu ba za ta je ba, saboda haka na ga ya kamata na kafa ƙungiyar don muryar mu ta je inda za a taimakawa masu wannan larurar ta sanƙarar mama. Saboda cutar na da tsananin wahala da kuma kashe kuɗi, ga kuma saka damuwa, don haka cutar ta da tsananin da duk wani mai tunani in dai ba ya samu kansa a ciki ba , to ba zai taɓa gane me ake nufi ba. Wannan ya sa na ga ya kamata na ga na yi iya yadda zan iya na taimakawa mutane, kamar yadda ni ma aka taimake ni. Saboda taimakon mutane da kuma gwamnati, da masoya na gabas da yamma kudu da arewa, har na samu aka zo ga wannan lokacin.
Ya ki ka tunkari lamarin ƙungiyar tun daga farko?
Gaskiya a wajen faɗi-tashi wajen samuwar wungiyar, tunanin farko da na yi, shi ne, a kan mai za a yi? Kuma da wanne irin kalamai za a je wa da mutane. To sai na ga ina da masaniya a kan cutar sanƙarar mama ɗin, don haka sai muka nemo suna daga wannan ɓangaren, har aka tsayar da wannan sunan da muka kiran ƙungiyar a yanzu. Kuma muna wayar da kan mata ne a kan yadda za su gano cutar da wuri don a samu mafita. Kuma a yanzu har an yi wa ƙungiyar rajista .
Da yake ciwon na mata da maza ne ko me ya sa Halisa Muhammad ta fi mayar da hankali a kan wayar da kan mata kawai?
To gaskiya mata su ne abin tausayi, sannan kuma sanƙarar mama, tana ƙara ci ne kamar wutar kara, don idan ka je asibiti abin zai ba ka tausayi, za ka ga yara ƙanana ‘yan shekaru 16 zuwa 18 an yanke mata nono ba manya ba ne. To ka ga dole ana buƙatar a wayar da kan mata don su gane ciwon ma akwai shi kuma gaskiya ne.
Kuma masu ciwon sanƙarar mama suna cikin wani hali wanda ba zai misaltu ba, saboda yanayin kula da lafiya da kuma magani, da abincin da za a ci abubuwa ne masu wahala, don ba ƙaramar kulawa suke buƙata ba. Duk abin da kika mallaka da na danginki sai ya kusa ƙarewa a kan wannan cutar wajen ceto rayuwarki, don haka ana cikin damuwa .
Kuma asibiti nan ne inda matsalar take, domin mu za ka ga a kowacce jiha asibitin koyarwa a nan aka duba masu rashin lafiyar sanƙarar mama ɗin. To mu dai a nan Jihar Kano, muna roƙo ga Gwamna Abba Kabir Yusif da ya taimaka mana a kan kayan gwaje-gwaje da sauran ayyukan da ake yi wa masu wannan cutar, don ba mu da injinan, har sai mun tafi wata jihar, wani lokacin mu tafi Abuja ko Maiduguri da Sokoto, sannan ake yi mana aikin. Kuma aƙalla shi wannan ciwon ana ɗaukar shekaru 3 zuwa 4 ana ƙarƙashin kulawar likita, wasu ma har ya kai shekaru 10 ma suna shan magani, don haka duk wanda ciwon nan ya same shi, ya samu kansa a cikin wata babbar jarrabawa. Sai dai mu roƙi Allah ya yaye mana wannan jarramawa da muke ciki.
Kuma fa ciwon sanƙarar mama na nan ƙauye da birni fiye da yadda ba a zato. Wannan ne ƙarfin kafa ƙungiyar don ta shiga har ƙauyuka wajen wayar da kan mata a wayar musu da kai a nuna musu ciwon sanƙarar mama gaskiya ne. Idan a baya ana yin magungunan gargajiya yana tafiya a yanzu ba haka ba ne. Zuwa asibiti a yanzu shi ne abu mai muhimmanci. Don a yi gwaje-gwaje a gano kina da shi, yadda za a ɗora ki a kan allurai da magani har a ga an cimma inda aka so a je.
Ko ta yaya ku ke samar da kuɗaɗen gudanar da ƙungiyar?
To a yanzu ni dai farko na sadaukar da kaina da rayuwata da lokacina gabaɗaya saboda masu cutar. Duk abin da nake yi a yanzu su nake tunawa, don ko abinci nake ci sai na tuna. Don akwai masu larurar da abinci ma ya gagare su samu. Don haka a yanzu, mutanen da suka saba taimakawa su ne dai za mu koma wajen su, don su ci gaba da taimakawa masu wannan larurar, domin suna buƙatar kayan abinci, magani, kuɗi na sayen allurai, haka nan suna buƙatar jini. Don haka muna neman taimako daga masu taimako da jini su je asibiti su bada jini su ce wannan na masu ciwon sanƙarar mama ne. Saboda ciwo ne da yake shan jini fiye da tunani. Don haka muke buƙatar taimako. Kuma muna buƙatar gwamnati da ta ɗauke mana nauyin wasu gwaje-gwaje da ake yi mana a ce kyauta ne. Idan an yi hakan ba ƙaramin adalci aka yi mana ba. Don shi wannan akwai wanda za ka ga wani dubu ɗari da hamsin, dubu ɗari biyu kuma kowanne da irin kalar magunguna da allurai da yake buƙata. Ka ga idan gwamnati ta ɗauke mana wannan, to an ɗauke mana abu mai nauyi a ciki, saboda shi wannan aikin duk bayan sati uku ake yi, kuma duk ranar da za a yi maka wannan aikin bayan ka sayi allurai da kayan gwaje-gwaje, za a fita ne da sassafe ƙarfe shida kana asibiti, don ka bi layi, kuma ba za ka dawo daga wannan gwajin ba tun da safe sai yamma wanda za a ɗauki tsawon shekara guda ana yi, sannan kuma sai a ɗora mara lafiya a kan gashi, sati uku-uku. Wasu za a yi musu sau takwas wasu har sau goma har zuwa sha biyu. Ya danganta da yanayin ƙonewar ciwon a jikin jini
Matsalar kayan gashi ba mu da shi a nan Jihar Kano. Akwai kuma wani gwaji da in an gama ake saka mutum a inji a ga da ciwon ko babu. To shi babu shi ma a Arewa gabaɗaya sai a Legas, duk waɗannan matakai sai an bi wajen ceton marar lafiyar. Don haka muna neman taimako daga masu kuɗi da ƙungiyoyin bada tallafi da kuma gwamnatocin jihohi da na tarayya da su bayar da gudunmawa domin wayar da kai da kuma kulawa ga masu ɗauke da wannan cuta ta sanƙarar mama, da take addabar mutane, musamman msta da suke raunana.
Daga lokacin da ki ka kafa wannan ƙungiyar zuwa yanzu an samu mambobi kamar nawa?
To ina ganin zuwa yanzu mun samu mambobi aƙalla sun kai guda 60 zuwa sama, ban da ma waɗanda suke mutuwa, don muna tattaunawa da junanmu a doshiyal midiya, kuma idan ta kama muna haɗuwa a gidana, don akwai su da yawa a Kano waɗanda suke wasu garuruwa su ne muke tattaunawar a onlayin sai mu haɗu mu yi tattaunawar mu a soshiyal midiya. Kuma a yanzu a yadda na shirya babu inda ba zan kai kukan mu ba mu masu wannan larura ta sanƙarar mama, zan shiga duk inda za a taimake mu a taimakawa rayuwarmu mu masu wannan larura ta sanƙarar mama. Kuma a yanzu ma muna ganin nasara, domin daga kafa wannan ƙungiyar na ɗora a soshiyal midiya mutane suka fara tambaya, har ma a yanzu duk wata manhaja tawa da nake amfani da ita a yanzu na mayar da ita da sunan sanƙarar mama, saboda kiraye-kirayen da muke yi ya je inda muke so ya je.
Domin ni na san irin matsala da kuma rashin hankalin da yake tattare da wannan ciwo, saboda tsadar magani da zirga zirgar zuwa asibiti, da ta abincin da muke ci. Don ni har gidana na sayar na wajen milyan tara a wannan cutar ga taimakon da ƙungiyoyi suka ba ni, ga gudunmawa da Gwamnatin Jihar Kano ta Abba Kabir Yusif ta yi mini duk don ceton lafiya ta, saboda haka wannan ciwo jarrabawa ce mai ƙarfi ga bawan da Allah ya ɗora masa wannan ciwo.
Don haka ina kira ina kuma ƙara kira ga hukumomin jihohi da na tarayya da ƙananan hukumomi da sarakuna da dukkan ƙungiyoyin jin ƙai, don Allah ku taimakawa masu wannan larura ta sanƙarar mama, duk abin da muke buƙata na wannan ciwo mu same shi da sauƙi ba sai mun je wani gari ba. Yanzu a ce Kano babu injin da za a yi mana aiki sai mun je Abuja ko Sokoto ko Legas, ai wannan ba ƙaramin ci baya ba ne, don haka a kawo mana agajin gaggawa mu masu wannan larura ta sanƙarar mama, muna buƙatar taimako, don haka a taimake mu a duk wata hanyar da muke buƙatar taimako, domin shi wannan ciwo a yanzu ya zama ruwan dare, idan babu shi a gidanka akwai a dangin ka ko a na kusa da kai, saboda shi wannan ciwo ya zama kamar wutar daji. Don haka ina kira ga duk wani wanda yake da hali, kamar manyan ‘yan kasuwarmu irin su Abdussamad Isyaka Rabi’u, Aliko Dangote, Aminu Dantata muna neman taimakon ku a kan wannan larura ta sanƙarar mama da muke fama da ita, don za mu zo gare ku har inda kuke mu kawo takardun mu na nemin taimako. Don haka muna neman taimakon gaggawa a game da halin da muke ciki, masu larurar sanƙarar mama muna cikin wani hali wanda mu kaɗai muka san halin da muke ciki, shi ya sa muka fito muke kira da babbar murya da a kawo mana agajin gaggawa. Cutar sanƙarar mama tana wahalarwa kuma tana kisa, kullum ƙara ci take yi kamar wutar daji, muna buƙatar taimako don ceto rayuwarmu. Allah ya kawo mana sauki gabaɗaya