Sallah: Tinubu na ƙoƙarin rage wahalhalun da ’yan Nijeriya ke fuskanta – Shettima

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya ce Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, na ci gaba da ƙoƙarin rage wahalhalun da ’yan Nijeriya ke fuskanta.

Shettima, ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, bayan idar da Idin Babbar Sallah da aka gudanar a filin Idi na Ramat Sƙuare da ke Maiduguri.

Ya ce tsadar rayuwa matsala ce da ta shafi ƙasashe da dama a duniya, sannan ya roƙi ’yan Nijeriya da su ƙara haƙuri da gwamnati.

A cewarsa, gwamnatoci a dukkanin matakai suna ɗaukar matakan rage wahalhalun da jama’a kw fuskanta.

Haka kuma ya yi kira da a samu zaman lafiya da haɗin kai a tsakanin al’ummar ƙasar nan, musamman a Jihar Borno da sauran sassan Nijeriya.

Dangane da zaɓen shekarar 2027, Shettima ya buƙaci ’yan siyasa su guji furta kalaman tunzura jama’a tare da gudanar da harkokin siyasa cikin haƙuri da mutunta juna.

Ya ce abin da ke haɗa kan ’yan Nijeriya ya fi ƙarfin abubuwan da ke raba su, yana mai cewa duniya ma tana fuskantar matsaloli da rikice-rikice, musamman yakin Gabas ta Tsakiya.

Bayan idar da sallar, Mataimakin Gwamnan Jihar Borno, Umar Kadafur, ya kai wa mataimakin shugaban ƙasa ziyarar gaisuwar Sallah.

Kadafur, ya yaba wa Shettima, bisa goyon bayan da yake bai wa gwamnatin da al’ummar Jihar Borno.

Ya kuma yi addu’ar samun ɗorewar zaman lafiya da ci gaba a Nijeriya, inda ya yi fatan gudanar da bikin Sallah cikin kwanciyar hankali a jihar.

By ukarofi