Sama da mutum 1,800 sun mutu a girgizar ƙasar Turkiyya da Siriya

Daga BASHIR ISAH

Aƙalla mutum 1,800 ne aka tabbatar sun mutu sakamakon girgizar ƙasar da ta auku a Turkiyya da Siriya.

Iftila’in wanda ya auku da safiyar Litinin, ya lalata wasu manya biranen Turkiyya, yankunan da galibin ‘yan gudun hijira daga Siriya ke da zama.

An ga masu aikin ceto na ta ƙoƙarin bincike don gano mutanen da ƙasa ta rufta da su.

Rahotanni sun ce wannan ita ce girgizar ƙasa mafi munin da aka fuskanta a baya-bayan a yankunan da lamarin ya shafa.

Tuni ƙasashe duniya irin su Chana, Indiya, Qatar, Amurka da sauransu suka bayyana ƙudirinsu na tallafa wa ƙasashen biyu a ɓangarori daban-daban dangane da halin da suka tsinci kansu.