Buhari ya sake naɗa Kashifu Inuwa shugaban NITDA

Spread the love

Daga ABUBAKAR M. TAHEER

Shugaban kasa Muhammad Buhari ya sake naɗa Kashifu Inuwa Abdullahi a matsayin Darakta-Janar na Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta Ƙasa (NITDA), sakamakon nasarorin da Hukumar ta samu bayan zaman Kashifu shugabanta.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne yayin ƙaddamar da shirin manufar ƙasa kashi na biyu a fadarsa ranar Alhamis.

Buhari ya ƙara da cewa, bayan dogon nazari da bibiyar ayyukan Hukumar NITDA ƙarƙashin Maikatar sadarwa da fasahar zamani, ƙarƙashin Kashifu Inuwa ya fahimci cewa hukumar ta cimma tarin nasarori wajen samar wa ƙasa cigaba.

“A kan haka ne na yaba da ƙwazon Hukumar ta NITDA, ni Shugaban Buhari na sake naɗa ƙashifu Inuwa Abdullahi a matsayin Shugaban Hukumar a karo na biyu daga shekarar 2023 zuwa 2027,” in ji shi.

Shugaba Buhari ya ƙara da bada haske kan gwamnatinsa wajen farfaɗo da tattalin arziki ta hanyar ma’aikatar sadarwa tun daga 2019 zuwa wannan shekarar ta 2023.

Ya kuma bayyana cewa faɗaɗa tattalin arziki duba da gagarumar gudunmawar da fasahar sadarwa ta zamani ta bayar a awu’on darajar kayyayakin amfani da ƙasa take samarwa (GDP) inda ya ba da kashi 18.44 cikin 100 a zangon na biyu a shekarar 2022, yayin da fannin man fetur ya samar da kaso 6.33 duk a lokaci guda.

NITDA ta Sami nasarori waɗanda ba za su misaltu ba wanda wannan shi ne dalilin da ya sa Hukumar take samar da cigaba da kuɗin shiga a kaso mafi tsoka a gwamnatin Shugaba Buhari.

By Editor