Ina ɗauke da cutar da mutane ƙalilan ne suka taɓa yin ta a duniya – celine Dion

“Cutar ta taɓa damar da nake da ita ta sarrafa muryata zuwa waƙa”

Daga AISHA ASAS

Rayuwa tamkar karatun boko ce, za ka fara tun daga lokacin da ka ke naziri, zuwa firamare, har ka kai sakandare, daga ƙarshe ka dira jami’a, inda duk wani karatun ƙarshe ta ke cibiyarsa. Duk wannan tafiyar idan ka yi ta, ba za ka iya dawowa baya ba, ma’ana ba zai yiwu kana jami’a ka dawo firamare ba, yin hakan zai sa a yi ma kallon mai tavin hankali.

Wannan shi ne ƙaramin misali akan rayuwa, duk ƙurciyarka wata rana za ka girma, kuma duk girmanka wata rana za ka tsufa.

Ɗaya daga cikin mawaƙa da duniya ta jima tana amo da rausaya da muryarsu, Celine Dion ta kasance mawaƙiya da har yau ba a samu wadda ta maye gurbinta a fagen masoya da kuma tasirin waƙoƙi.

A ‘yan watanin baya duniya ta rikece da ce-ce-kuce kan yanayin rama da mawaƙiyar ta yi fiye da ƙima, ramar da za a iya danganta ta da ciwo. Tuni mutane suka dinga jifar mawaƙiyar da cutuka daban-daban, yayin da hotunan mawaqiyar suka ƙara shiga kafafen sada zumunta wasu hotunan har da na ƙarya, masoya da mabiyan ta suka ƙara shiga ruɗani, sai dai duk da haka mawaƙiyar ta yi gum da bakinta, bata kare kanta kan duk irin jifar curuta da ake yi mata ba, sai dai ta yi wata ‘yar gajeruwar magana, da ta fi kama da ta haushi, inda ta ce jikinta ne kuma ba abin da ya dami mutane da ramar da ta ke yi.

Sai dai a ‘yan kwanakin nan Celine Dion ta karya azumin shiru da ta ke yi na lamarin lafiyarta, inda ta yi magana kan lamarin a wani faifan bidiyon da ta saki a shafinta na Instagram. Mawaƙiyar ta fara da ba wa masoyanta haƙuri kan shiru da suka ji tare da bayyana yadda ta yi kewar kasancewa da ma’abuta son waƙoƙinta.

“Ina mai ba ku haƙuri kan yadda na ɗauki tsayin lokaci ba ku ji ni ba. Matuƙa na yi kewar kasncewa tare da ku a fagen waƙa. Kamar yadda ku ka sanni, ba ni da ɗabi’ar ɓoye-ɓoye, sai dai akan wannan lamari, a baya ban shirya iya yin magana kansa ba ne, sai dai yanzu zan yi, don na shirya sanar da ku halin da nake ciki.

Na jima Ina fama da matsala da ta shafi lafiyata, kuma abin yana da girma, ba ni da ƙarfin zuciyar da zan iya karɓar abin har in samu ragowar da zan iya fuskantar ku, in sanar da ku halin da na ke ciki, wannan ne ya sa ba ku ji daga gare ni ba tsayin wannan lokaci.

Likitoci sun tabbatar Ina ɗauke da wata cuta da ba kasafai ake samun masu ita ba, domin cikin kashi miliyan kashi ɗaya ne kawai suka tava kamuwa da ita. Don haka har yau muna kan neman sani game da cutar, sai dai muna da tabbacin ita ce silar duk matsaloli da canjin da jikina ya samu.

Abin baqin ciki, wannan cuta ta tava kaso mafi yawa na rayuwata, don wani lokaci Ina samun wahalar yin tafiya, kuma ta kan tava damar da nake da ita ta sarrafa muryata zuwa waƙa.

Don haka, Ina mai baƙin cikin sanar da ku cewa, ba zan samu damar yin yawon nishaɗantarwa na ƙasashen Turai da zan gudanar a watan Fabrairu ba. A halin yanzu akwai ƙwararrun likitoci da suka haɗa kai wurin ganin sun taima min na samu lafiya. A ɓangare ɗaya, akwai ‘ya’yana abin alfahari na da ke iya yin su wurin ba ni ƙwarin gwiwa.

Ina matuƙar ƙoƙari ta ɓangaren atisaye tare da malama ta, ba don komai ba, sai don shauƙin ganin na sake komawa kan dandamali Ina nishaɗantar da ku. Sai dai Ina so ku sani, ba abu ne mai sauƙi ba, sai dai abinda na sani, waƙa ita ce abinda na yi duk tsayin rayuwata, kuma ita ce abinda na fi son yi.”

Celine Dion ta yi ɗan shiru, yayin da ƙwalla ta fara ziyartar kogon idonta, kafin ta ci gaba da cewa, “Ina matuƙar kewar kasancewa da ku, Ina kewar yi maku waƙa masoyana. Sai dai a halin da nake ciki yanzu hakan ba zai samu ba. Ba abinda ya kamace ni face tunkarar neman lafiya, kuma Ina da yaƙinin nan da bada jimawa ba, za mu kasance tare.”

Daga ƙarshe Celine Dion ta miƙa godiya ga masoyanta kan irin damuwa da suka yi da lamarin ta, kuma ta jinjina masu kan irin soyayyar da suka nuna mata tare da alhinin rashin lafiyar ta.

Wacce ce Celine Dion?

Bakanediyar mawaƙiya da aka haifa a wani ƙauye da ake cewa, Quebec, a garin Charlemangne, kilomita 50 tsakanin sa da Montrea. An haife ta a ranar 30 ga watan Maris, 1968, a asibitin Le Gardeur.

Celine Marie Claudette Dion na ɗaya daga cikin mawaƙan da suka fito daga gida mai yawan zuri’a, domin ta kasance ‘ya ta 14 a gidansu. Ta samo sunanta na Celine ne albarkacin waqar wani mawaƙin Faransa mai suna Hugues Aufray, wadda ya sa mata ‘Celine’.

Idan muka koma ga tarihin gidansu Celine Dion, za mu fahimci cewa, waqa ba tsinta ta yi a ƙasa ba, domin rubuta waƙa da rerewa ya kasance gadon gidansu.

Tun daga iyayenta zuwa ‘yan’uwanta suna yin waƙa a wani gidan baƙi da ya kasance mallakinsu. Don haka tun tasowar ta kunnuwanta suka saba da jin iyayenta da ‘yan’uwanta na waƙa. A ranar 18 ga watan Agusta, 1973, wanda ya kasance ranar auren ɗan’uwanta mai suna Michel, ta kasance rana ta farko da Celine Dion ta tava yin waƙa a bainar jama’a, inda ta yi waƙa mai taken ‘Du fil, des aiguilles et du coton’.

Tun daga wannan lokaci ta ke yin waƙa a gidan baƙin nasu, jefi-jefi, sai dai irin yadda jama’ar da ke zuwa wurin suka kamu da ƙaunar muryarta ya sa aka ware mata lokaci na musamman da ta ke yin nata waƙoƙi.

A irin wannan yanayi, kaset ɗin da aka naɗi waƙoƙinta ya faɗa hannun wani sanannen manajan mawaƙa, a lokacin tana da shekaru 12. Kuma a cikin waƙoƙin akwai wadda mahaifiyarta mai suna Therese ta rubuta, mai suna ‘Ce n’etail qu’un reve’ sai kuma ɗan’uwanta da ita kanta.

Take Rene ya ayyana nasarar da muryar tata zata iya samu idan ta shiga duniya. Kamar kowa, ya kamu da son murya, sai dai shi ya fahimci tsantsar baiwar da ke tare da ita, don haka ne ma ya yi kasadar jinginar da gidansa, don ya yi amfani da kuɗin wurin fitar da kundin waƙoƙinta na farko da aka sanya wa sunan waƙar ta ‘Ce n’etail qu’un reve’.

Tun daga wannan lokaci nasara ta yi sallama a ƙofar mawaƙiyar, inda a kowane kwanan duniya cigaba ta ke gani a tafiyarta. Yana ɗaya daga cikin nasarar da ta samu, iya fitar da wani sabon kundi shekara ɗaya bayan fitar na farko, kuma a shekarar ta yi nasarar lashe kambun zinari na mawaƙa, a bikin fitattun mawaƙan duniya, wato Yamaha World Popular Song Festival. A watan Oktoba 31, na shekarar 1982.

Shekara ɗaya bayan haka, aka zaɓi mawaƙiya Celine Dion ta wakilce Ƙasar Kanada da waƙarta ta ‘D’amour ou d’amitie’ a ranar kasuwar waƙa ta MIDEM, wato International Market of the Disk and the Musical Publishing, a Cannes.

Celine Dion a halin rashin lafiya

Kuma a shekarar ne ta zama mawaƙiya Bakanediya ta farko da ta taɓa amsar gambun zinari na Golden Disk a Faransa, da waƙar ta ‘D’amour ou d’amitie’ bayan da waƙar ta siyar da kwafi har 700, 000. Wannan ya faru a 1 ga watan Satumbar shekarar.

Daga nan kuma muryarta sai ƙara saurin tafiya ta ke yi, inda cikin ƙanƙanin lokaci ta zagaye duniya, kuma ta shiga jerin fitattun mawaƙa da duniya ta yarda da waƙoƙinsu, hakan ya sanya cigaba ta ɓangaren ciniki da karramawa ba a maganar su, domin ta kasance a bakunan duk wani taro na mawaƙan duniya da za a yi.

Tun daga shekara ta 1985, ta fara yawon waƙa tsakanin Kanada da Faransa, daga bisani ta ke zagaye ƙasashen Turai gabakiɗaya. Kowacce shekara akan shelanta inda mawaƙiyar zata yi waqa a zahiri tsakanin ƙasashen, yayin da mutane za su yi ta cincirodin cika wurin don samun damar ganin fitacciyar mawaƙiya mai maƙogaron zinari, Celine Marie Claudette Dion .