Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Sanatoci daga jihar Kebbi da suka haɗa da Sanata Yahaya Abubakar Abddullahi na gundumar mazaɓar Kebbi ta Arewa da Sanata Garba Musa Maidoki na mazaɓar Kebbi ta Kudu sun gana da shugabannin sojoji dangane da matsalar tsaro da ke addabar waɗansu sassan jihar.
Sanata mai wakiltar mazaɓar Kebbi ta Arewa Dr Yahaya Abdullahi ya jagoranci sanatocin jihar Kebbi a ofishin shugaban samar da tsaro na ƙasa Manjo Janar Christopher.
Sanata Yahaya Abdullahi ya ce wannan ziyarar tana da alaƙa da rashin tsaro da ke addabar jihar Kebbi musamman yankin gundumar mazaɓar Kebbi ta Kudu don nemo yadda za a shawo kan matsalar ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane a yankin.
‘Yan majalisar dattawan sun nemi Janar Christopher da ya ɗauki matakin gaggawa wajen ganin an kawar da matsalar garkuwa da mutane da kuma yawan kisan gillar da ake yi wa al’ummar yankunan.
Wannan yana daga cikin ayyukan wakilcin da su ke yi wa alu’ummar da suka bi dare da rana suka zaɓo su don su wakilce su, ba sun zo Abuja ba ne don shan shayi ba sun zo ne wakiltar al’umma kuma a matsayinsu na dattawa duk abinda ya taɓa mutanen su suma ya tava su saboda haka ba za su zauna ba har sai sun ga an nemo hanyar magance wannan matsalar.
Manjo Janar Christopher ya bayyana sanatocin a matsayin dattawa da ya kamata sauran shugabanni su yi koyi da su saboda sun nuna halin dattako da ke nuna matsalar al’ummar su ce a gabansu.
Shugaban samar da tsaron Manjo Janar Christopher ya bayyana cewa hukumar samar da tsaro shirye take wajen ganin ta yaƙi yan ta’adda da kuma masu garkuwa da mutane a sassan ƙasar nan da ke addabar al’umma.