San’insa tsakanin Naziru da Rarara: Rashin alƙiba ne ke kawo irin wannan cece-kucen – Malam Khalid Musa

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano 

A abinda ya bayyana na rikici da san’insa da ke wakana tsakanin Naziru M. Ahmad da aka fi sani da Naziru Sarkin Waƙa da Adamu Dauda Kahutu Rarara, abin ya yi ƙamari ne a shekarar 2023 inda a wata hira da tashar DCL ta yi da Naziru Sarkin Waƙa ya bayyana cewa, an bashi miliyan 150 da motar mliyan 80 don ya bar tafiyar Atiku Abubakar, inda Rarara ya fito ya ƙaryata Naziru a kan wannan furuci inda ya nuna cewa wannan ba abu ne mai yiwuwa ba sam.

Wanda daga bisani Naziru ya fusata ya mayar masa da zazzafar martani, to tun daga wancan lokaci ne tataɓurza ta fara har zuwa wannan lokaci, inda takan taso lokaci bayan lokaci.

Ko a kwanan nan ma waccan cacar bakin ta ɓarke a wannan karon a kan tsadar mota ne, wannan ya ce tashi tafi tsada wancan ya ce ta shi ta fi.

A bincike da Manhajar ta gudanar ya nuna cewa mafi yawan kace nace ɗin magoya bayansu ne suke rura wutar rikicin. 

Naziru ya ce, yana karewa yaronsa ne, wanda ya ce anyi masa Rarara ya yi wa yaronsa gori shi ne ya nuna motar ya ce idan Rarara ya isa ya sayi irinta.

Malam Khalid Musa jigo ne kuma uba a masana’antar fim ta Kannywood, kuma memba a Kannywood Foundation, Blueprint Manhaja ta ji ta bakinsa inda ya bayyana cewar wannan taƙaddamar da Naziru da Rarara suke yi a matsayin cacar baki marar amfani.

Yana mai cewa abin da hakan ke nunawa shi ne rashin alƙibla a rayuwarsu ko kuma wanda ya damu da hakan a cikinsu. Abin da ya kamata su yi gasa a kansa shi ne da me jama’a ke amfanuwa da su? Wanne taimako suke bayarwa cikin al’umma? Mutum nawa ne suka gina su wa alheri da ya jibinci rayuwarsu?.

Ya ƙara da cewa, “Yawancin manyan ‘celebrities’ na ɗaukar wani muhimmin abu da za su rinƙa yi a duniya da ya taɓa rayuwar wasu raunana amma banda mu, mene ne amfanin gasar hawa mota mai tsada? Amfanin me za ta yi wa al’umma? Abin alfahari shi ne mutum nawa na taimakawa? Makarantu nawa na gina? Yara nawa na ɗauki nauyin karatun su? Mutane nawa ake ciyarwa a kowacce rana.”

Sannan ya ja hankalinsu da cewa “Ina fatan Rarara da Naziru za su karkatar da hankulansu zuwa ga abinda zai zamo albarka ga rayuwarsu, su tuna cewa gobe kiyama Allah SWT zai tambaye su ne abinda su ka yi da dukiyar da suke alfahari da ita, ba zai tambaye su mota nawa su ka saya ba, ina taya su addu’ar Allah ya tsare su faɗawa cikin gargaɗin (Alhekumul takasur)” inji Malam Khalid.

Ko ma dai mene ne masu lura da al’amuran yau da kullum na ganin akwai buƙatar su maida hankali wajen ciyar da Arewa gaba ta fannoni daban-daban da Arewa ke buƙata, ba gasar motocin miliyoyin Nairoru ba da kuɗin za su iya tallafa wa al’umma da dama a yankin mu na Arewa.

By ukarofi