Sanusi Rikiji ya fito takarar cike gurbin Majalisar Dattawa a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Zamfara Rt. Hon. Sanusi Garba Rikiji ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar Sanatan Zamfara ta tsakiya gabanin zaɓen cike gurbi da za a yi a jihar.

Idan za a iya tunawa, Gwamna Bello Muhammad Matawalle ya naɗa Sanata Hassan Muhammad Nasiha wanda yake wakiltar yankin a matsayin mataimakin gwamnan jihar.

Rikiji wanda ya riqe muƙamin kakakin majalisar dokokin jihar na tsawon wa’adi biyu, har zuwa lokacin da ya bayyana tsayawa takarar cike gurbin kujerar Sanata Hassan Muhammad Nasiha, shi ne shugaban ma’aikata na kakakin majalisar wakilai, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila.

Hon. Sanusi ya ziyarci hedikwatar jam’iyyar APC ta jihar da ke Gusau a hukumance domin nuna girmamawa ga shugabannin jam’iyyar APC na jihar, inda ya bayyana sha’awarsa a kan wannan matsayi a ranar Laraba da ta gabata.

Ya shaida wa jiga-jigan jam’iyyar APC na jihar a ƙarƙashin jagorancin Hon. Tukur Umar Ɗanfulani cewa, yana son ya zama ɗan majalisar dattawa ne domin ya ƙara ba da gudummawar sa ga ci gaban siyasa da tattalin arzikin jihar.

Hon. Sanusi Rikiji ya kuma bayyana cewa yana da niyyar ƙara tabbatar da kyakkyawan wakilcin da sanatoci da suka gabata suka yi a zauren majalisar dattawa ta ƙasa don kawo sauyi mai ma’ana a Jihar Zamfara.

“Niyyata ta tsayawa takarar Sanata a zaɓen cike gurbi mai zuwa ita ce, in taimaka tare da goyan bayan ƙoƙarin Gwamna Bello Mohammed Matawalle wajen fuskantar ƙalubalen tsaro da ke addabar jihar tare da haɗa hannu da gwamnan wajen ganin an sake kafa sabuwar Zamfara,” ya ce.

Ya gode wa shugabannin jam’iyyar na jihar bisa tarbar da aka yi masa, ya kuma yi alƙawarin ci gaba da biyayya ga jam’iyyar da shugabancinta domin ci gaban jihar.

Da yake mayar da martani, shugaban jam’iyyar APC na jihar Zamfara, Hon. Tukur Umar Ɗanfulani ya bayyana farin cikinsa kan yadda mai neman tsayawa takarar Alh. Sanusi Rikiji ya bi tsarin da ya dace wajen bayyana aniyar sa.

Ɗanfulani wanda ya yi wa baƙon nasa fatan alheri ya bayyana cewa a matsayinsu na shugabannin jam’iyyar ta APC a Jihar Zamfara, sun sha alwashin yin adalci ga dukkan mambobin jam’iyyar.

Ya ci gaba da cewa, al’ummar Zamfara sun cancanci wakilci nagari kuma jam’iyyar za ta haɗa kai da jama’a wajen ganin an tallafa wa wanda ya fi kowa a majalisar dattawa a madadinsu.