Sarkin Ƙabilar Ibo na Kafanchan ya jinjina wa Sarkin Jama’a bisa haɓɓaka zaman lafiya

Spread the love

Daga ABUBAKAR LABARAN a Kafanchan

Sarkin Ƙabilar Ibo mazauna garin Kafanchan da kewaye, Maigirma Richard Ogbonna ya jinjina wa Mai Martaba Sarkin Jama’a Alhaji Muhammadu Isa Muhammadu saboda hovvasarsa dangane da harkokin da suka shafi jaddada zaman lafiya.

Richard Ogbonna ya yi wannan jinjinan ne a saƙonsa na fatan alkhairi jim kaɗan bayan da aka kammala bukukuwan cika shekaru 25 a karagar mulki da sarkin ya gudanar a garin Kafanchan.

Sarkin Ibon ya qara da cewa Sarkin Jama’a bai taɓa yin ƙasa a guiwa ba dangane da al’amurran da suka shafi zaman lafiya mai ɗorewa a ƙasarsa da kewaye.

Ya ƙara da bayyana wa wakilin Manhaja cewa, Sarkin Jama’a ya nuna ƙwazo a tafiyar da al’amurran mulki inda ya kawo ci gaban ƙasarsa, da haɗa kan al’umma tare da baki mazauna ƙasar.

Richard ya jaddada cewa halayen Sarkin Jama’a ya tabbatar da irin abubuwan da ake buƙata na ci gaba, dalilin da ya sa Sarkin Ibon ya yi kira da ya ci gaba da kawo irin waɗannan sauye sauyen da za su tabbatar da daula mai kyau domin kowa da kowa yayi walwala.

Ya ƙara da cewa Sarkin Jama’a ya kawo ababan jin dadin rayuwa ga mutanen masarautarsa, da dawwamammen zaman lafiya tsakanin dukkan al’ummomin dake masarautarsa, ta hanyar mulkin adalci da yake yi.

Sarkin Ibon ya ce koda yake yankin Kafanchan da kewaye, ta yi fama da fuskantar tashin hankakali da rikice-rikice a baya, Sarkin Jama’a ya yi ƙoƙari matuƙa domin ganin zaman lafiya dawamamme ya dawo ƙasar dalilin da ya sa cigaba da harkokin arziki suna bunƙasa sosai a ƙasar Jama’a a yau.

A ƙarshe, Sarkin Ibon, ya yi kira ga al’ummarsa da su ci gaba da harkokinsu a cikin zaman lafiya da lumana tsakaninsu da sauran abokan zamansu da na cinikayya.

By Editor