Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Ƙungiyar Ƙwadago (NLC da TUC) ta gargaɗi Gwamantin Tarayya kan ƙin biyan ma’aikata tallafin N35,000 da ta yi musu alƙawari duk wata kan cire tallafin mai.
Ƙungiyar Ƙwadago ta yi gargaɗin ne a lokacin da take zargin Gwamnatin Tarayya da saɓa alƙawarin da ta yi na biyan ma’aikata N35,000 na tsawon wata shida domin rage raɗaɗin cire tallafin mai.
Shugaban ƙungiar TUC, Festus Osifo bayyana cewa ma’aikata sun shaida musu cewa sau ɗaya kaɗai gwamnatin ta biya N35,000 daga lokacin da Shugaba Tinubu ya sanar da matakin.
Ya ce savanin alƙawarin biyan kuɗin da Tinubu ya yi, a watan Satumba kaɗai Gwamnatin Tarayya ta aka biya ma’aikatanta kuɗin, in banda wasu tsiraru da suka samu daga baya.
Da yake magana bayan taron gaggawa da suka yi a Abuja a ranar Talata, ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da na jihohi da su yi ɗamarar biyan ma’aikata kuɗaɗen, kamar yadda gwamnatocin suka jima suna buƙatar ma’aikatan da su yi haƙuri.
