Sasanci tsakanin Hausawa da Fulani zai magance matsalar tsaro a Arewa

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Ashe matsalar tsaro da ake fama da ita a Arewa, na da nasaba da kisan ƙare dangi da Fulani ke yi wa ƙabilar Hausawa? Tun da ake samun ƙalubalen tsaro a jihohin Arewa maso yammacin Nijeriya tsakanin Fulani makiyaya da Hausawa manoma, ban taɓa kawo wannan tambayar a raina ba, don ina ganin ba batun kisan ƙare dangi ba ne, tsohuwar rigima ce da aka saba fuskanta tsakanin manoma da makiyaya, ƙalubalen ɗumamar yanayi da ya kai ga cinye burtalolin shanu zuwa filayen gonaki, da kuma uwa uba shigar ɓata gari cikin harkar satar shanu da garkuwa da mutane.

Amma a ranar da na shiga zauren sada zumunta na clubhouse a nan ne na ci karo da wani ɗaki da ake tattaunawa game da wannan matsala ta yawaitar hare-haren ta’addanci da ‘yan bindiga ke kaiwa ƙauyukan jihohin Zamfara, Sakkwato, Katsina, Kaduna, Naija da wasu yankunan babban birnin tarayya Abuja. Ga mamakina dukkan mutanen da ke cikin tattaunawar su kusan ɗari ɗan Arewa ɗaya ne, sai kuma ni da tsautsayi ya shigar da ni a lokacin. Na zaci zan ga tattaunawar ta haɗin gwiwa ce tsakanin Musulmi da Kiristan Arewa ko dai wasu ɓangarori na Nijeriya, musamman ma dai daga jihohin da abin ya shafa. Amma sai na ga akasin haka, zallar ‘yan Kudu ne kawai suke sharhi suna faɗar son ransu, har da wani masanin tarihi a cikin su da ya dage yana ba da tarihin mamayar da ƙabilar Fulani suka yi wa garuruwan Hausawa a Nijeriya ta Arewa.

Ko da ya ke tattaunawar mu da su ba ta yi nisa sosai ba, don ina shiga suka yi ca a kaina ganin cewa ni ɗan Arewa ne, saboda yadda suka ga hotona sa ye da kaftani da hula. Na yi ƙoƙarin bayyana musu abin da na fahimta da ƙalubalen tsaro da ke faruwa a Arewa, amma sam su yadda tunanin su ya nuna musu da yadda ‘yan bokonsu da ‘yan siyasar su ke gaya musu, shi ne daidai, sai muka kasa fahimtar juna, har ma da waɗanda ke zagina da kirana sunaye. Saboda kawai fahimta ta ta sava da tasu, alhalin ni ɗan Arewa ne kuma mazaunin Arewa, su kuwa ina ganin da wuya in a cikin su wani ya zauna a Arewa, ko kuma iyakacinsu Abuja.

Babu shakka na yi baƙin cikin wannan abu da ya ke faruwa a jihohin Arewacin qasar nan, da ma sauran sassan Nijeriya, saboda hare haren ta’addanci, sace-sacen mutane da satar shanu da duk ake danganta su da al’ummar Fulani. Kasancewa ta na fito daga tsatson Fulani a ɓangaren uwa da kuma Bahaushe a ɓangaren uba. Ko ta wanne ɓangare ina tsakiya, kuma babu wanda zan iya nesanta kaina da shi, don jinina ne. Amma zan iya nesanta kaina da irin ayyukan da suke gudanarwa marar kyau.

Tashar BBC Eye, masu gudanar da binciken sirri game da abubuwan da ke faruwa a ɓoye wanda sauran ‘yan jarida ba sa ba da rahotonsa a cikin labaransu. Ko kuma rashin sanin dalla dallar wasu bayanan da ba kasafai ake jin su ba. Sun gudanar da wani shiri da suka sanyawa suna ‘The Bandits Warlords of Zamfara’ a Turance, wato Shugabannin Mayaƙan ’Yan Bindiga na Zamfara wanda wani ɗan jarida da ya kira kansa da suna Yusuf ya gudanar da bincike a kan abubuwan da ke haddasa rikicin Fulani da Hausawa a Jihar Zamfara. Binciken nasa ya bankaɗo wasu abubuwa da dama wanda su ne suka ja hankalina ga son yin wannan rubutu.

Ko da ya ke kafin zuwan BBC Eye dazukan Zamfara, wakilin jaridar Daily Trust Abdul’Aziz Abdul’Aziz shi ya fara yin wannan tattakin zuwa jihar domin ganawa da wasu shugabannin mayaƙan Fulanin daji ƙarƙashin jagorancin sanannen ɗan bindigar nan Bello Turji, inda cikin rahoton da ya shirya mai taken Sharing The Shade With Turji wato Inuwa Ɗaya Tare Da Turji ya bayyana ƙorafin da ya haddasa waɗannan Fulani da ake yi musu kallon gidadawa, suka zama abin tsoro da damuwa a Nijeriya.

Waɗannan rahotanni guda biyu sun haifar da ayoyin tambaya da dama daga ‘yan Nijeriya, tare da tayar da muhawara game da makomar ƙasar nan, da yadda za a kawo ƙarshen waɗannan fitintinu. A nan ba ina son sake wata sabuwar bita kan abubuwan da rahotannin suka ƙunsa ba ne, amma ina son sake kai hankalin mu ga ƙorafe-ƙorafen da ake kawar da kai daga gare su, don a zauna a dubi matsalar da idanun basira.

Kamar yadda aka karanta ko aka saurara daga bakin waɗannan ‘yan bindiga da aka tattauna da su sun bayyana cewa zalunci da rashin samun kulawar gwamnati, danniyar sarakunan ƙauye da tavargazar ‘yan banga a kan waɗanda ba su ji ba ba su gani ba, na daga cikin dalilan da suka sa su ɗaukar makami su nuna damuwarsu, kafin lamarin ya munana har ya koma neman kuɗi, sata da ta’addanci, da faɗan kin jinin wani jinsi.

Babu wani mai aiki da hankali da zai yarda da cewa abubuwan da ake yi na ta’addanci ya dace ko yana da kyau, sam-sam. Kuma lallai ne masu faɗa a ji a tsakanin Fulani da hukumomin gwamnati su tsaya tsayin daka sai an magance wannan matsala, a kuma kawo ƙarshen hare hare na ƙeta da mugunta da ake kai wa mazauna karkara da ƙauyuka, da cin mutuncin mata da ƙananan yara.

Ɗaukar makamai don neman awatar ’yanci da sunan ƙabilanci, yana da haɗari sosai. Duba da irin yadda ya faru a wasu ƙasashen Afrika irin su Somaliya, Saliyo, Laberiya, Rwanda, Sudan da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da sauran su. Faɗan ƙabilanci da wata ƙabila ke zargin wata ƙabila da tauye mata haƙƙi, yana da matuƙar haɗari sosai, musamman a irin ƙasar da muke ciki, mai ƙabilu daban-daban. Kuma lallai a kiyaye aukuwar hakan, saboda makomar ƙasar nan.

Sannan lallai gwamnati ta yi abin da ya kamata wajen duba koke-koken waɗannan mutane, tare da samar da mafita da ba za ta tauye haƙƙin kowa ba, don inganta rayuwar Fulani da sauran ƙabilun Nijeriya da su ma suke kuka da rashin ko in kula da matsalolin da suke fuskanta. A daina bari, sai lokacin da mutane suka ɗauki makami, suka fara haifar da ɓarna sannan ne za a nemi a zauna da su. Bayan sun gano daɗin ɗaukar makami su yi fashi, su sace shanu da dabbobin mutane, su karɓi miliyoyin kuɗi da sunan kuɗin fansa.

Zarge-zarge da ake yi wa wakilan gwamnati ko jami’an tsaro na nuna fuska biyu da yaudara a tattaunawar da ake yi da su, ya kamata a daina. Gwamnati ta nuna da gaske ta ke yi, wajen samar da tsaro da zaman lafiya a ƙasar nan. A ɗauki tsauraran matakai na daƙile yadda wasu vata gari da ba Fulani ba, suke shiga cikin ayyukan ta’addanci, musamman a ɓangaren satar mutane da hari a wuraren ayyukan haƙar ma’adinai da cinikin makamai da ƙwayoyi.

A makon da ya gabata Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai ta Tarayya, Ahmad Idris Wase, sai da ya kusa zubar da ƙwalla, yayin da ya ke ganawa da manema labarai, yana bayanin yadda ‘yan ta’adda suka mayar da ƙauyukan da ke mazavarsa ta Wase a Jihar Filato kufayi, saboda yadda suke yawan kai hare-hare kusan a kowacce rana, cikin ‘yan watannin nan.

A yayin da nake wannan rubutun mahara da ake zargin Fulani ne, sun sake kai hari kan mazauna ƙauyen Pinau da ke cikin ƙaramar hukumar Wase, sun kashe baban wani abokina Malam Usman da wasu mutane da maraicen ranar Laraba. Yayin da ɗan uwan abokin nawa har yanzu ba a gano inda ya ke ba.

Abubuwan da ke faruwa a kudancin Jihar Filato na neman sake mayar da jihar baya, bayan rigingimun ƙabilanci da faɗan manoma da makiyaya a shiyyar Arewacin jihar ya haifar da asarar dukiya da rayuka masu yawan gaske.

Da fatan Ubangiji Allah zai kawo mana ƙarshen wannan musiba ta ta’addanci da ta addabi arewacin Nijeriya, ya haɗa kan ƙanƙanin mu Hausawa da Fulani, su dawo zaman tare cikin girmamawa da kula da haƙƙoƙin juna.