Arewacin Nijeriya: Tauyayyun Zakuna (2)

Daga MUHAMMAD NASEER LERE

Kamar yadda na bayyana mana irin halin da muka tsinci kan mu a arewa a kashi na farko, har na kawo yadda masu yi mana aikace-aikace da biya mana buƙatu na yau kullum suka rikiɗa, suka koma masu nema mana mafitar yanayin da ko dabbobi da gonakin Arewa bai ƙyale ba. Sannan na tsakura muku yadda suka yanke cewa za su fito su nuna irin yadda aka siyasantar da harkar tsaro a yankin Arewa. Wataƙila sun zavi wannan matakin ne domin sun san cewa, ‘yan Arewa suna da hakkin rayuwa cikin annashuwa da walwala kamar yadda kowa yake yi a yankin sa.

Wannan mataki ya ƙara tabbatar da cewa, lokacin da za su fito da ainahin surar su, tare da amsa sunan mahaifiya me tautsayi ya yi a Arewa. Domin kowa ya san yadda mahaifiya ke damuwa da lamarin jaririnta, kowa ya san cewa jariri ya fi samun kulawa da tausayawa kaso 79% a gun mahaifiya, duk da cewa ba ita ce kawai ke da haƙƙin bayar da kulawar ba.

A wannan fannin ma kusan hakan ne, wai mata ne suka fito zanga-zanga, ko ina kawai za ka ji ana cewa, mata sun yi zanga-zanga a kano, duk da ba wannan ce zanga-zanga karon farko a kano ba, amma na san ko zanga-zangar wyamatar fyaɗe da ‘yanuwa mata suka yi a kano ban ji an kira su da wata kalma mummuna ba. Ita kuwa wannan zanga-zangar sai kawai lokaci guda wasu masana suka fara cewa, ai duk wanda ka gani cikin zanga-zangar, ko dai ‘yar yawon ta zubar, ko kuma ‘yar kwangilar yahudu. Ko waye yahudun? Oho.

Lokaci guda bayan an kammala zanga-zangar rana ta farko, komai ya kara girmama. Masu zagin ‘yan zanga-zangar suna zagi, masu yabo da nuna cewa wannan zanga-zangar abu ne me kyau, amma ba za su fito ba, suma sai suka ƙara yawaita. Babban ɓangaren da ya fi bawa zanga-zangar karsashi, shi ne ɓangaren ƙungiyoyi masu zaman kansu, da suka nuna suna shirye domin mara wa zanga-zangar baya, ba wai iya mara baya ba suna shirye a ƙara fita zanga-zangar tare da su.

Musamman vangaren lauyoyi irin, Abba Hikima, da kuma ire-iren Bulama Bukarti. Duk wani cece-ku-ce da gidajen radiyo da jaridu suka yi tayi bau bawa zanga-zangar armashi kamar bayyanar su ciki ba. Abu biyu da zuwan su ciki ya samar shi ne, cire wa masu zanga-zangar tsoro, da kuma sanya wa masu son dakatar da zanga-zangar tsoro. Wataƙila masu son ganin bayan zanga-zangar sun ɗauka ana tafiya ne kara-zube, amma sai ga wani sabon nizami a ciki. Nan take suka zura idanu, yayin da ita kuma gwamnati take ganin wannan zanga-zangar za ta iya zama haɗari, ko barazana ga ‘yan ƙasa.

Kamar koyaushe ita gwamnati daman aikinta shi ne, dakatar da duk wani abinda zai zamo barazana ga ‘yan ƙasa, hakan ya sa dole gwamnati ta yi iya abinda za ta iya koda bai dace ba, don ganin an dakatar da abinda ka iya zama barazana ga tsaro. Ba wai ta fito fili tace, ku daina zanga-zanga ba ne. Ba kuma ta harba bindiga ne ta ce, bat a buƙatar ganin kowa a zanga-zangar kamar yadda ta saba yi wa duk wata zanga-zangar da ka iya kawo barazanar tsaro ba. A wannan fannin ta yi ‘yan dabaru ne irin wanda duk wata gwamnati keyi wajen ɗalile abinda bata so. Ba wai so nake na ce Gwamnati ba ta fahimci inda zanga-zangar ta dosa ba ne, ta sani sarai.

Sannana ba buƙatata in faɗa muku irin yadda ta yi dabarun ba ne, ba kuma cewa na yi bata saka ƙarfin damtse ba. domin ko a Katsina da zaria jami’an tsaro sun kama wasu daga cikin masu yin zanga-zangar. Abinda nake so a fahimta shi ne, yadda zanga-zangar ta juye bayan an ayyana ta a zahiri. Da yadda ‘yan Arewa suka kalle ta, da kuma yadda gwamnati da ƙungiyoyi masu zaman kansu suka kalle ta, shi ne abinda nake so a fahimta. Zanga-zangar ta juye zuwa zanga-zanga mai matuƙar tasiri. Su kuma ‘yan arewa sun fahimci zanga-zangar a matsayin siyasa ko zanga-zangar kawo ƙarshen gwamnati, ita kuma gwamnati ta kalli zanga-zangar a matsayin wacca za ta iya juyewa zuwa ta’addanci, su kuma ƙungiyoyi sun fahimci zanga-zangar a matsayin jarumta, da faɗa da cikawa.

Kun fahimta? Akwai banbanci tsakanin furucin za mu fito zanga-zanga, da kuma fitowa zanga-zangar. Misali, “za mu fito zanga-zangar Asuu Strike” kamar yadda ɗalibai suke faɗi tsahon watanni ba su fito ba. Da kuma “Za mu fito zanga-zangar Secure North” kamar yadda mata masu kishin Arewa suka faɗi ‘yan kwanaki kaɗan suka fito. Kun fahimci bambancin? Bari na ƙara bayani, su ɗaliban jami’a sun ɗau tsawon lokaci suna maganar zanga-zanga amma ba su yi ba. Ko sun yi, bata da armashin da za a kira ta zanga-zangar ƙasa. Su kuma mata masu kishin Arewa cikin kwanakin da suka ambaci za a yi zanga-zanga, a cikin kwanakin suka fito suka yi zanga-zangar da za a iya kiranta fiye da ‘national protest’.

Wannan faɗa da cikawa da suka yi shi ne ya bawa lamarin armashi, shi ne kuma ya karkato da hankalin gwamnati a kan lamarin, har ta iya gane cewa, wannan lamarin zai iya zama ta’addanci. Har akwai masu jera zanga-zangar da zanga-zangar ‘EndSars’. Sannan wannan fitar rashin tsoron ne ya, bawa wasu damar shiga cikin lamarin duk da cewa suma lamarin ya shafe su, amma sun ƙarfafa lamarin a ƙungiyance ne, saboda irin na macen ƙoƙarin da waɗannan zakuna suka yi.

Wannan shi ne zai ƙara tabbatar maka da cewa waɗannan iyaye matan ba ƙaramin namacen ƙoƙari suka yi ba. Domin yadda suka shelanta za su fito ɗin kawai, jarumta ce mai zaman kanta. Ballantana fitowarsu tituna duk da cewa, sun san irin miyagun kalaman da za su fito daga bakunan wanda suka fito domin su ɗin. Duk da cewa, sun san ‘ya’yan cikinsu za su iya kiransu karuwai, hakan bai kashe musu guiwa suka kasa fitowar ba. Ba iya zagi ba, wallahi dukkansu sun san cewa, za a iya biyan matasa ₦500 su sassare su. Haka dai labari ya bazama cewa, an yi zanga-zangar lumana, wacce take kira da a kawo ɗauki wa yankin Arewacin Nijeriya. Taken zanga-zangar shi ne, a bawa yankin Arewa tsaron da aka rantse da Ƙur’ani da Baibul za a ba su.

Yanzu mu yi tunani a matsayinmu na ‘yan ƙasa. Misali, yanzu tunda har gwamnati ta fahimci abinda ake nufi da zanga-zangar menene abinda yakamata gwamnati ta yi? Duba lamarin za ta yi, ko kuma dai aikawa da gaisuwar mutuwa za ta yi? Ai wanda aka kashe ya riga ya riga mu gidan gaskiya, amma me za a ce wa iyalinsa? Ko kuma me za a yi domin kare su daga bindigar data kashe iyayensu. Wannan shi ne abinda ya sa zanga-zangar ta cigaba da gudana duk da irin ƙalubalen data fuskanta ciki da waje. Abu ɗaya kawai shi ne, shin abinda Zanga-zangar ke kira aka yi za ayi ne, ko kuma wani abun daban? Ina nufin shin gwamnati ba za ta iya tsare yankin arewa ba, eh, ko a’a?

Shin idan za a magance matsalar tsaron, yaushe za a yi? idan kuma ba za a yi ba, yaushe za a faɗa wa ‘yan Arewa cewa ba za a iya tsare rayukansu ba? Wannan shi ne kawai amsar da masu zanga-zangar suka buƙata. Ko gun gwamnatin ko gun waye ma. kawai dalilin da zai jefa babban yanki irin Arewa cikin wannan tashin hankalin, da kuma dalilin da zai sa ɗan Arewa ba zai runtsa ido ya yi barci cikin salama ba. Amma kawai sai aka ƙi fahimtarsu, da gwamnatin da ‘yan arewan, duk sai suka kasa fahimtar abinda zanga-zangar ke kira a kai. Maimakon a taimaka a faɗa musu amsar abinda suke kira akai, sai kawai mutanenmu suka zavi jifansu sunaye irin, ‘yan yawon ta zubar. Duk da cewa, cikinsu akwai waɗanda suka haife duk wani ɗan shekara 20. Kuma wallahi ba wai da gasken ba su fahimta ba ne, sun fahimta sarai. Kawai kamar yadda na faɗi ne, lamarin ya saɓa da tunanin wasu ne, amma abinda zanga-zangar ke kira a kai a bayyane yake yadda babu wanda zai ce bai fahimta ba.

Abinda zanga-zangar take kira akai, ya yi dai-dai da abinda mawaƙi Dauda Kahutu Rarara ya kira talakawa a shekarar 2015 inda ya ce, “Maza da mata, ku fito talakawa ga zaɓe ya kyautu mu zo neman ‘yanci”. In ba a manta ba, talakawa sun amshi wannan kira na wannan mawaƙi domin lokacin idanun talakawan sun rufe wajen neman yanci. In za ku tuna tun kafin gwamnatin su Rarara ta kafa mulki, Rararan yake kira ga talakawa da su bijire wa gwamnati me hula, shin kun taɓa jin gwamnatin lema ta gayyaci Rarara ofishin DSS, ko kuma ta kama shi bisa zargin ya kira talakawa neman ‘yanci, kamar yadda akai wa masu zanga-zangar?

A iya sanina, ko harara ba a yiwa Rarara ba. Sai dai ma lambobin yabo da ya samu gurin talakawa, da kuma kyautatawa ta ɓangaren Jam’iyyar Maja ta wancan lokacin. Amma su laifin waɗannan iyayen namu shi ne, sun fito sun yi kira da a bawa talaka ‘yancin rayuwa, koda cikin baƙin talauci ne, matuƙar zai rayu cikin ahalinsa. Sai suka zama manyan masu laifin da za a iya kiransu ai musu barazana ko a tsorata su. Ko saboda basu shiga sutudiyo ne ba, kamar yadda su Rarara sukai oho.

A nan zan so mu amsa wannan tambaya, don Allah idan idanuwan ‘yan Arewa za su rufe saboda kashe-kashen da yankin Arewa ya samu daga 2013-2015, menene dalilin da zai sa idanunsu ba zai rufe ba duk da cigaban kashe-kashen daga 2015-2021? Dalili ko da guda ɗaya ne ina son sani. Domin ni a tunanina, duk rai sunan sa rai, in kuma an rasa shi, duk sunan hakan mutuwa. Da wanda aka saka mishi bam, da wanda aka biyo shi gida aka yanka duk sunan su matattu. Idan hakan gaskiya ne, menene dalilin da zai sa wancan fitowar ta 2015 ta zama jihadi a gun mutanen Arewa, amma wannan kuma zai zama yawon ta zubar? Ko saboda wannan mata ne waɗanda suka fi iblis makirci suka shirya, wancan kuma maza masu ƙarfin zuciya kamar Putin na Rasha ne suka shirya?

Kafin mu samu amsa, bari mu waiwaya baya. In baku manta ba, na tuna muku yadda aka fara tattaunawa a kan halarcin zanga-zanga a muslunci, da kuma haramcin fitowa ga mace. Tun wancan karon bawai naqi yin dogon bayanin a kan hakan ba ne, kawai masu cewa hakan ne nake tunanin ƙwaƙwalensu akwai ciwon mantau, tunda sun iya manta zanga-zanga kala-kala waɗanda aka gudanar shekarun baya.

Domin yi wa kowa adalci za mu iya tambayar su, shin ya matsayin zanga-zangar da aka yi watan mayun shekarar 2003? Sannan ya matsayin zanga-zangar da akayi shekarar 2011 wacce ta yi sanadiyar kashe rayuka masu yawa? Sannan ya matsayin shahararriyar zanga-zangar nan wacca ta shige cikin kundin tarihi me taken ‘OccupyNigeria’ wacce aka yi gangaminta a shekarar 2012? Idan har zanga-zanga zunubi ne, da har zai iya zama lasisin fasikanci, ta ya babu wanda ya zama fasiƙi ko ɗan yawon ta zubar a wancan lokacin.

Za mu iya cewa duk wata zanga-zanga a ƙasar nan koyi ake da mai girma shugaban ƙasa. Duk da na ga masu fassara zanga-zangar ‘securenorth’ da fassarar son rai! Suna ikrarinsu ‘yan gani a bigensa ne. Yana da kyau su koma su duba tarihi. Indai kuwa zanga-zangar ‘OccupyNigeria’ za ta shige cikin kundin tarihi, to wajibi zanga-zangar ‘Securenorth’ ita ta samu shafuka a tarihin.

Sannan indai waɗanda suka shirya suka fito zanga-zangar OccupyNigeria ba su zama fasiƙai, ko masu son tada zaune tsaye ba, to wajibi a goge waɗannan sunayen akan wadanda suka shirya suka fito zanga-zangar Securenorth. Sannnan indai waɗancan abinda sukai sunansa jarumta, to suma waɗannan dole a kira su zakuna!

Saboda haka za mu iya cewa, babu wani wanda ya nuna haramcin zanga-zanga a wancan lokacin, kawai yanzu ta zama haramun ne saboda tasirinta ya bayyana gazawar ulul’amrinsu. Sai kuma dalili na biyu, ya kamata ku lura da kyau, akwai masu ɓoye tsoronsu a bayan addini. Idan suna tsoron yin abu, kawai sai su ƙaƙaba wa addini su ce addinin ne ya ce. Bamu sani ba, amma tabbas babu addinin da zai ƙyamaci zanga-zanga fiye da zub da jinin ɗan adam.

Zaku iya tunawa na ce akwai waɗanda suke tambayar ta ya zanga-zanga za ta kawo mafitar rashin tsaro a Arewa? Su ne ya kamata mu duba, domin ko ba komai sun tambayi mafita ne, ba ƙalubalantar mafitar ba. Sun e Ya kamata na fahimtar das u cewa, wannan fushin da zakunan mata suka gwada ba wai fushin kwana 1 ko sati ɗaya ba ne. Fushi ne wanda suka ƙunshe cikin zuciyarsu tsawon shekaru 7.

Na sani, a cikin mutanenmu, akwai waɗanda suka ji waqar “Mun Shiga Next Level” wacce aka yi shekarar 2019. Wataƙila sun ji baiti na biyu na cewa “Welkom tuza nex labul, ga ta mun ganta a fissiful”. Idan ba a manta ba, a shekarar 2019 da talakawa ke cin moriyar wannan waƙar, masu garkuwa da mutane sun shiga wata makarantar kimiyya a Dutsin-ma, inda suka sace matar aure da wasu yara. Ba iya wannan ba, an yi ta ɗauki ba daɗi da ‘yan ta’addan a hanyar Kaduna zuwa Abuja a ita wannan shekarar da aka kira ‘Fisful’.

Shin tsammaninku, waɗannan masu zanga-zangar tun wancan lokacin abin baya damun zuciyarsu? Ko Lokacin da kuke jin waccan waƙar su sun san cewa babu wani abu mai suna “Fisful” a Arewa. Kawai babu yadda suka iya ne, ba za su iya dakatarwa ba, saboda komai a Arewa sunansa siyasa. Wannan shi ne ya sa suka ƙara haƙurin shekara 3.

Wannan zanga-zangar ita ce kawai suke ganin ko gwamnatin za ta fahimci, yankin Arewa har yanzu jini na zuba, har yanzu babu wani zaman lafiya, zaman lafiyan iyakarsa a waƙa ne kawai. Kenan indai zanga-zanga zai iya kawo canjin gwamnati babu abinda zai sa ba zai kawo tsaro a yanki kamar Arewa ba, matuƙar litan man fetur bai fi ran ɗan adam a Arewa ba.

Tun farko ba wai tambayar zanga-zanga zai kawo mafita ne abin yi ba. Kamar wanda yake cikin ambaliyar ruwa ne, sai kawai ga jirgi ya zo dab da shi, shin zai kama jirgin ya hau ne, ko zai tsaya tambayar inda jirgin ya nufa? Kusan haka ne, kamar yadda bashi da wani fatan cigaba da rayuwa cikin ambaliyar, haka muke rayuwa a Arewa. Kenan in an zo da wani lamarin da bai sava hankali ba, ba za mu haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen binsa ba, sai dai mu mu yi ajalinsa ta hanyar tsine masa? Wannan abin haushin kuna tsammanin zai samu gurbin zama a zuciyar mace duk da kun yi shaidar ita halitta ce me rauni?

Sannan a ƙarshen wannan zangon, zan so masu ganin zanga-zangar ba za ta iya zama mafita da su fahimci wani abu. Ita wannan zanga-zangar da kuka ga rana tsaka an shirya ta, ana tsammanin ita ce kawai hanyar da ba a gwada ba wajen nuna halin da yankin Arewa ke ciki. An yi taron manema labarai babu iyaka, an buga a jarida babu iyaka, an yi interview da waɗanda ake kashe musu ahli babu iyaka. Amma kullum lamarin sai ƙamari yake. Shi yasa suka ce bari su gwada hanyar zanga-zangar ko Allah zayisa gwamantin ƙasar ta fahimci halin da Arewa ke ciki. Za mu runtsa a wannan maƙalar, idn Allah (T) ya nufa muna da rai, za mu numfasa i zuwa gaba.

Muhammad Naseer Lere ɗan ƙasa ne mai bayyana ra’ayi. 0701 485 0068

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *