Sharhin littafin ‘Jiki Magayi’

Daga KABIRU YUSUF FAGGE (ANKA)

Sunan littafi: Jiki Magayi
Marubuta: John Tafida Umaru Zariya da Rupert East
Shekarar Bugawa: 1995
Maɗaba’a: Northern Nigeria Publishing Company (NNPC)
Bugawa: Ahmad Bello University Press, Samaru, Zaria
Yawan Shafuka: 52
Mai Nazari: Kabiru Yusuf Fagge (Anka)

Jiki Magayi labari ne na wani ƙasurgumin kuma shahararren attajiri mai suna Mallam Shaihu mazaunin cikin birnin Galma. Saboda yawan kuɗin Mallam Shaihu ba inda sunan shi bai kai ba (shafi na 1). Kai hatta shi kan shi Mallam Shaihu bai san yawan dukiyarsa ba (shafi na 2).

Sai dai kash! Duk da tarin dukiyar Mallam Shaihu, Allah bai taɓa ba shi haihuwa ba, ya yi aurarraki don samun haihuwa, amma bai taɓa samu ba. Haka nan ya ɓatar da dukiya ba adadi a wajen malamai da bokaye da ‘yan bori duk don neman maganin haihuwa, amma ko ɓatan wata ba a taɓa samu a cikin matansa ba.

Damuwar Mallam Shaihu ta rashin haihuwa ta yawaita wanda har ta kai shi ga yin mafarki da wata yarinya a gidan Mallam Audu mai suna Zainabu, wanda a mafarkin aka yi masa isharar idan ya aure ta lallai zai sami haihuwa.

Mallam Shaihu bai yi ƙasa a guiwa ba ya tuntuvi malamin duba da tsubbu a kan mafarkin da ya yi. Malamin ya duba masa, ya ba shi labari zai auri wata yarinya ‘yar gidan Mallam Audu ɗin, kuma za su haihu, sai dai auren yana cike da wahala da da-na-sani, ya ba shi shawarar ya haƙura da batun auren.

Mallam Shaihu ya yi ta tunani dangane da wannan al’amari, amma saboda son haihuwa ya shure maganar malamin kasa, ya sa aka kira masa Mallam Audu don neman auren ‘yarsa.

Yarinyar da Mallam Shaihu ya gani a mafarki ita ce Zainabu, sai dai tana da wanda take so, don haka ko da mahaifin Zainabu wato Mallam Audu ya zo gare shi ya sanar da shi cewa:

“Wannan magana tana da wuya, domin kuwa ita Zainabu, tun suna ƙanana akwai wani yaro sunansa Abubakar tare suka taso, tana sonsa, shi kuma yana son ta, har kuwa kowa ya sani ita zai aura…” (Shafi na 3).

Duk da haka Mallam Shaihu bai gamsu ba ya ci gaba da neman auren Zainabu, har a wajen malamin duba. Mallam Shaihu ya nemi yardar Zainabu, amma ta ƙi, don ya cimma burinsa sai ya sa wani shahararren malamin tsubbu mai suna Mallam Sambo ya yi masa aiki a kan yarinyar wanda ya juye mata hankali ta dawo gare shi. Ta rabu da saurayinta Abubakar wanda aka yi musu ‘baiwa’ da shi.

Mallam Shaihu ya auri Zainabu bayan ya saki guda daga cikin matansa. Wannan abu ya tunzura Abubakar ya sha alwashin ɗaukar fansa, ya ludire cewar in har a kan ɗa ne aka yi masa haka, to zai yi maganin da sai albarkar da yake nema ga ɗan ta zama la’ana. Hakan ya sa, ya shiga faɗi-tashi tsakanin bokaye da wahalar duniya a garuruwa, har sai da ya samo maganin da ya je, wanda a lokacin Mallam Shaihu da Zainabu sun haifi yaron kirki mai suna Abdullahi ana kiransa Kyauta, ya yi masa magani, yaron ya zama fitinanne kuma kasurgumin barawo har ya haɗu da wani shahararren ɓarawo mai suna Dogon Yaro.

A ƙarshe a yawon yin sata har Kyauta ya je yin sata garin da mahaifinsa ya gudu, kuma gidansa tsautsayi ya sa, ya kashe uban.

Sharri ɗan aike, kuma alhaki kwikwiyo mai shi yakan bi, bayan mutuwar Mallam Shaihu, mahaifiyar Kyauta; Zainabu ta gaya wa ɗanta wanda ya yi masa asiri ya zama barawo. Wannan ta sa Kyauta ya yi nadama kuma ya doshi Galma don ɗaukar fansa a wurin Abubakar. Sai dai kash! Lokacin da ya isa Galma, har wajen Abubakar ɗin, ya tarar da shi yana cikin tsananin rashin lafiya, ko da shi Abubakar ɗin ya gan shi sai ya ce: “Ka makara! Wata fansar sai gobe ƙiyama.” (shafi na 49) sai ya tuntsire ya mutu. Saboda yana cikin tsananin rashin lafiya.

A ƙarshe Kyauta ya koma Ganye don ɗauko mahaifiyarsa. Dukiyar mahaifinsa kuwa bayan an yi mata ƙima an cire ushura aka damƙa masa komai. Ya tara dukkan malaman garin don yi wa ubansa addu’a ya raba musu ita. Haka ya rabar da kuɗi da kayayyakin mahaifinsa da takarce da dabbobi. Suka dawo Galma shi da mahaifiayrsa, anan ma aka ba shi gado, ya bai wa mahaifiyarsa, shi kuma ya yi sallama da ita don barin garin domin ya tafi neman rage alhakin da ya ɗauka. Ya fita daga shi sai sandarsa da gafaka da ‘yar buta.

Babban jigon littafin ‘Jiki Magayi’ shi ne, “neman/son haihuwa”, domin waɗannan dalilai:
Misali a shafi na biyu, marubutan littafin sun ce:

“Shekararsa ashirin da yin aure amma bai tava haihuwa ba. Ya yi aure da yawa, kullum gidansa ba a rasa matan aure huɗu. Ya vatad da dukiya ba iyakawajen malamai da bokaye da ‘yan bori garin neman maganin haihuwa, amma cikin matansa babu wadda ta taɓa ko ɓatan wata. Ko yaushe idan ya tuna da wannan babbar hasara ta rashin da sai ransa ya dugunzuma..”

Haka a wannan shafin, a mafarkinsa sun ce:
“Godiya tana gidansa har ta haifa masa ɗan duƙushi kyakkyawa…”
A shafi na uku (3)

“Amma don tsananin son da ya maida duk wannan ba a bakin kome ba idan buqatarsa ta biya.”

A shafi na takwas (8) an sake fito da jigon dai. “….kuma ka cika aure-aure da yawa, duk wadda ka aura kuwa idan kuka yi ‘yan shekaru ka ga ba ta haihu ba sai ka sake ta da cin zarafi…”

A shafi na sha uku (13): “Dalili dai yana son ɗa ne, an kuwa gaya masa idan ya auri yarinyar nan zai samu…”

A shafi na sha huɗu (14): “To, tun da yake kwaɗayin ɗa ne ya sa ya yi mini wannan abu…”

A shafi na 17 ma an bayyana jigon: “….sa’an nan zai ga kwansa…”

“Zainabu ta sami ciki….” Shafi na takwas ke nan da sauransu.

Ƙananan Jigogi:

Bayan babban jigon “neman haihuwa” littafin ‘Jiki Magaji’ yana da ƙananan jigogi masu mara masa baya kamar:
Ɗaukar fansa,
Sata,
Bokanci

Ɗaukar Fansa – mun ji yadda Abubakar ya sha alwashin ɗaukar fansar ƙwace masa masoyiya da Mallam Shaihu ya yi, shi ya sa ya nemo maganin da ya sa cansa Kyauta ya zama ƙasurgumin barawo.

Haka shi ma Kyauta da ya sami labarin wanda ya yi masa magani har ya zama varawo, ya sha alwashin zuwa don ya ɗauki fansa a kan Abubakar.

Sata – Kyauta ya zama ƙasurgumin ɓarawo tun yana yaro, har ya bar gida, ya je garuruwa yana sata – ta dalilin sata ya haɗu da ƙasurgumin varawo mai suna Dogon Yaro, kuma ta dalilin sata ya kashe mahaifinsa.

Bokanci/Tsubbu – waɗannan suna cikin ƙananan jigo na labarin ‘Jiki Magayi’ – domin tun a farko-farkon labarin mun ji yadda Mallam Shaihu ya rinƙa batar da dukiya mai yawa a wajen malamai da bokaye da ‘yan bori wajen neman haihuwa (shafi na biyu, sakin layi na 1).

Bugu da ƙari da malamin duban ƙasa ya yi amfani wajen juyo da hankalin Zainabu gare shi (shafi na 6)
Shi ma Abubakar ya shiga duniya ne neman shahararren malami don ɗaukar fansa (shafi na 11). Kuma har ya riski malamin mai suna Tausayinka-Da-Sauki wato Zakari (shafi na 12) wanda daga jin sunan ka san boka ne.

Wurare Da Garuruwa:

A cikin littafin ‘Jiki Magayi’ marubutan sun yi amfani da garuruwa kamar irin su: Birnin Galma, Yale, Dawan Rukuki, Sanga, Rimi, Garuje da sauransu.

Ƙa’idojin Rubutu:

In ban da amfani da wasu daga tsoffin salon ƙa’idojin rubutun Hausa da marubutan suka yi, to a littafin an kiyaye ƙa’idojin rubutu yadda ya kamata. Misalan tsoffin ƙa’idojin rubutun sun haxar da:

 • Kwantad da maimakon kwantar da
 • sanad da maimakon sanar da
 • sayad da maimakon sayar da
 • sa’ad da maimakon sa’ar da
 • garimmu maimakon garinmu
 • Halimmu maimakon halinmu
 • lalle maimakon lallai
 • izni maimakon izini
 • ko me maimakon komai
  Sai kuma wajen da suke rubuta sunayen lokuta da ƙananan baki. Ban da waɗannan lallai marubutan sun yi ƙoƙarin kiyaye ƙa’idojin rubutu.

Sannan akwai wani abin dubawa a littafin, duk irin tafiye-tafiye da yada zango da shiga garuruwa da wasu taurarin littafin suka yi ba a nuna inda suka yi salla ba ko sau ɗaya – sai dai kawai an ambaci sunayen sallolin Azahar da La’asar a matsayin lokaci kawai.

Haka nan yanayin littafin ya fi kama da fassara.