Shekaru masu rauni a rayuwar matasa

Daga MARYAM BATOOL

Girma ya kan fara daga shekara 15 har zuwa 20. Matasa a wannan lokacin su kan faɗa cikin wasu mawuyatan halaye ko kuma rashin sanin inda suka dosa. A irin wannan lokutan ne suka fi buƙatar fahimta, kula, rangwame da shawarwari daga gurin magabatansu, ’yan uwa, abokai da al’umma gabaɗaya.

Damuwa tana daga cikin manyan abubuwan da matasa su kan samu kansu a ciki, wanda matsaloli, kamar talauci, rashin aikin yi, rashin zuwa makaranta, fargabar makaranta (jarrabawa, kuɗin makaranta da sauransu), rashin fahimtar juna tsakanin iyaye, saɓani a cikin abokantaka da kuma waɗanda suka fuskanci wani zalunci, kamar fyaɗe, duka, tsangwama tsakanin abokai da ’yan uwa, har ma da soyayya.

Wasu matasan kuma sukan jefa kansu cikin damuwa, saboda tunanin makomar rayuwarsu da tsoron nasara ko kuma rashin ta. Wasu kuma sukan damu da kamanninsu da zubin jikinsu, wanda suke gwadawa da na sauran abokansu, waɗanda suke ganin kamar sun fi su. Ko kuma ma daga irin abokansu ma na yanar gizo da kuma shahararrun mawaƙa, ’yan fim ko ’yan ƙwallon ƙafa da suke koyi da su. Hakan sai ya kawo musu tantama a tsakanin su kansu, ya zama cewar, duk wani abu da za su yi, sai su ga kamar ba za su iya ba ko kuma ba su cancanta ba. Wato sun rasa ƙwarin gwiwa a rayuwarsu kenan.

A irin wannan yanayin ne komai ya kan iya faruwa duk da kuwa tarbiyyar da iyaye su kan gina su a kai, sai ya zama zuciyarsu a buɗe ta ke ga duk wani abu da za su yi, don ganin sun bar halin da suke ciki ko kuma sun samu abinda suke so.

Shaye-shaye na ɗaya daga cikin irin waɗannan mugayen halaye, wanda kashi 40 a cikin 100 na matasa sukan samu kansu a ciki. Wasu su kan warke daga halin, wasu kuma ya zama sanadiyar gurɓatar rayuwarsu.
Shaye-shaye kaɗai ya kan janyo munanan abubuwa, wanda a halin yanzu suke addabar al’umma; sata, ta’addanci, ƙwace-ƙwace, fyaɗe, banda cututtukan da ya ke haifar wa masu yi, sannan ya rusa ’yan’uwantaka da addini.

Wasu zamani ne ya ke ruɗar su a dalilin rashin sanin muhimmancin kansu, musamman mata su na ganin ya zamar musu wajibi su yi abun da sauran matasa irinsu suke yi ko da kuwa ya kaucewa al’ada da addini, don dai kawai su burge. Daga nan ne kuma ƙiyayya, kishi da baqin ciki suke fara ɗarsuwa a zukatansu, domin ba wai kawai burgewar suke so su yi ba, a’a, har ma su ga sun fi wasu ko kuma sun yi fice a cikin harkar.

Matasa da yawa kuma sukan faɗa ƙangin soyayya, wanda bai zama lallai ma soyayyar ba ce kulawar da ba su samu ba suke nema daga wajen masoyan nasu, ko kuma son a ɗauke su da muhimmanci, wanda idan aka samu akasin haka, sai su fara ganin rashin muhimmancin kansu, wasu lokutan su ga ba su da amfani ma gabaɗaya a duniyar.

Daga haka ne wasu suke samun munanan ra’ayoyi, sai su samu kansu cikin ɓacin rai da son vata wa kowa rai, sai su riƙa yin wasu abubuwan da bai kamace su ba kuma har su fara jin haushin iyayensu, saboda sun kasa magance musu matsalarsu. A wasu lokutan ma har abun ya kai ga su na so su ƙarar da rayuwarsu, wato su kashe kansu.

Saboda haka a irin wannan shekarun, matasa taimako suke buƙata da tausa. Faɗa, hayaniya ko duka ba zai sa su daina abun da suke yi ba, illa iyaka ma ya ƙara tunzura su, su aikata wata ɓarnar. Amma da yawa sai manyan su zama sune suke assasa abun, maimakon su gyara, saboda a tunaninsu yara ne ba su san komai na daga rayuwa ba.

Duk da cewa, manyan suna da nasu matsalolin, bai kamata su riqa nuna cewar, matsalar matasan ba wata matsala ba ce, idan aka haɗa da tasu, su na mantawa da ƙwaƙwalwar matasan ba irin tasu ba ce, kuma sannan juriyarsu da tunaninsu ba iri ɗaya ba ne.

A yanzu haka babu matsalar da ta kai rashin fahimtar juna tsakanin babba da yaro, inda sai ka ga har a cikin aji malamai suna kasa jituwa da ɗalibansu, yayye da ƙanne suna samun saɓani a tsakaninsu har ma ya kan kai ga iyaye.

Kamar yarda aka ce, sarki goma zamani goma, su ma matasan suna canjawa da zamani, kuma a kullum ƙalubalen ƙara ƙaruwa suke, kuma a na ƙara samun wayewar kai da bai zama lallai manyan su fahimta ba. Abun da ba a yi a nasu zamanin ba, sai kuma ya zama yayi a wannan zamanin, abun da manyan za su ga hauka ne da ɓata a lokacinsu, su kuma hankali ne da cinyewa a nasu zamanin.

Matasa da suka samu kansu a cikin waɗannan halaye, nutsuwa ya kamata su yi, su tambayi kansu; shin wannan halayen da suke ciki, za su samar musu da mafita a rayuwarsu? Shin abokan da suke tare da su, za su amfane su ta hanya mai kyau? Me suka tanadar wa rayuwarsu kuma wanne irin misali za su bar wa duniya a kansu?

Su zama masu kyautata zato akan matsalolinsu da kuma mutane gabaɗaya, su riƙa yin abubuwa masu muhimmanci, waɗanda za su sa su ji cewa, su ma suna da muhimmanci kuma sun aikata abu mai kyau.

Za su iya bin hanyoyi masu sauƙi wajen gusar da ɓacin ransu, kamar tafiyar ƙafa maras nisa a waje mai ni’ima kuma mara hayaniya, karatu ko rubutu, idan masu ƙaunar yi ne, kallo, wasanni, hira da sauran abubuwa masu ɗebe kewa.

Sannan matasa su bambance abun da ya ke da amfani a rayuwarsu da kuma wanda ba su da shi, su yi ƙoƙarin yin masu amfanin kafin su yi na ƙasa da su.

Abu na ƙarshe sannan kuma wanda ya ke da matuƙar muhimmanci shi ne, sana’a; ba lallai sai wani abu babba ba ko mai tsada ko kuma ma a ce sai an buɗe shago ba. Idan babu yiwuwar haka, za a iya mayar da abun da ake so ya zama abun yi ko abun sayarwa.

Misali; idan mace mai son kwaliyya ce, sai ta koyi yadda za ta yi na kuɗi ko kuma ta riƙa sayar da kayan kwalliyar ta yadda ba zai yi mata wahala ba kuma sana’ar ba za ta gundire ta ba, saboda da ma can tana da sha’awa a kai tun asali!