Shettima da Idris za su halarci ƙaddamar da littafin babban editan ‘Leadership’ a Abuja

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Mai girma mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima zai zama babban baƙo a taron ƙaddamar da littafin ‘Writing for Media and Monetising It’, wanda babban editan jaridar ‘Leadership’, Azu Ishiekwene ya wallafa kuma maɗaba’ar buga littafai ta ‘premium times’ ta buga, don samun lada ga rubutattun abubuwa masu kima.

Ministan yaɗa labarai da haɗin kan ƙasa, Alhaji Idris Muhammed shi zai jagoranci ƙaddamar da littafin wanda za a yi a ranar Laraba, 26 ga watan Yuni, 2024 da misalin ƙarfe 10 na safe a ɗakin taro na Yar’adua Centre da ke Abuja.

Mawallafin tare da maɗaba’ar sun ce, bayan makonni da aka ɗauka ana nazari a kan littafin gami da yi masa gyare-gyare, zai shigo kasuwa domin mutane su mallaka saboda amfana da shi, don haka su ke farin ciki.

Sauran waɗanda za su halarci taron sun haɗa da; tsofaffin gwamnoni, da shuwagabannin hukumomi da ministoci da ƙungiyoyi masu zaman kansu da makamantansu.

Leave a Reply