Daga AISHA ASAS
Mai karatu barkanmu da sake kasancewa a shafin Kwalliya na jaridar Blueprint Manhaja. Sannunku da jimirin bibiyar mu.
Na san mai karatu zai iya ɗan saka alamar tambaya kan darasin namu, wato kalamar ‘takalma mai kyau’. Idan tunaninka ya tafi kan tsari na kyau da ake gani a zahiri ne, to ka dawo baya, hakan zai sa ka fahimci inda darasin namu ya dosa.
Takalma masu kyau da muka ambata na magana ne kan takalma masu bada lafiya, ba masu wahalar da ƙafa ba.
Akwai takalma da muke wa laƙabi da ‘orthopedic shoes’ su musamman an gina su ne da zumar ba wa ƙafa damar walwala da taimakonta wurin ganin ta inganta. Siffar waɗannan takalma kuwa ita ce laushi a inda ake takawa. Don haka ne masana da dama suke ba wa marasa lafiyar ƙafa shawarar saka takalma masu laushi.
Idan muka auna hakan a mizanin hankali, a duk lokacin da ka saka takalma masu laushi tafiya komai nisanta saidai ta haifar da gajiya ga jiki baki ɗaya har ƙafar sakamakon ka yi fiye da yadda za su iya ɗauka, amma ba ƙaraf ce zata dinga zugi ita kaɗai ba ko zafi.
Idan kuwa inda ake takawa na takalman na da ƙarfi to fa ko ba doguwar tafiya ka yi ba ƙafar na iya fara ciwo, wannan kuma babbar matsala ce ga ƙafar idan hakan ya cigaba.
Masana orthopedic sun yi gargadi mai tsauri kan yawaita amfani da takalma marasa kyau.
Sun ce takalman da ke matse yatsu ko kuma waɗanda ba sa bai wa tafin ƙafa kariya kan jawo ciwon tafin ƙafa, kumburin yatsu, lalacewar jijiyoyi da sauyin tsarin tafiya. A cewarsu, waɗannan matsaloli kan kai ga ciwon baya da gwiwa saboda yadda jiki ke rasa daidaiton tafiya ta uwa mai ɗauke da shi wato ƙafa.
Masana sun bayyana cewa, takalmi mai kyau na nufin takalman da suka dace da girman ƙafa, ma’ana ba wanda ya matse ba, kuma bai yi ƙaranci ga tsawo ba. Sannan su kasance masu laushi wanda zai ba ƙafar kariyar da ake buƙata.
Sun kuma gargaɗi mata masu yawan sanya takalman ‘high heel’ wato takalma mai tsini na tsawon lokaci.
A cewar Dakta Kabiru Lawal: “Dogon amfani da takalma mai tsayin diddige na ƙara matsin lamba ga yatsu da gwiwoyi. Wannan na iya janyo matsalolin kasusuwa daga baya.”
