Shugaba Xi Jinping ya zanta da Biden ta kafar bidiyo

Daga CMG HAUSA

Da daren ranar yau Jumma’a ne shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya zanta da takwaransa na ƙasar Amurka Joe Biden ta kafar bidiyo.

Xi ya ce, tun da suka yi shawarwari karo na farko ta kafar bidiyo a watan Nuwambar bara, zuwa yanzu, an samu wasu sabbin manyan sauye-sauye a faɗin duniya. Zaman lafiya da samar da ci gaba, na fuskantar babban ƙalubale, duniya na fama da rashin kwanciyar hankali da tashe-tashen hankali.

Ba ma son ganin ɓarkewar rikici a ƙasar Ukraine. Abubuwa da dama sun sake shaida cewa, bai kamata a yi fito-na-fito ta fuskar soja ba a ɓangaren alaƙoƙin ƙasa da ƙasa, kuma yin taho-mu-gama bai dace da muradun kowane ɓangaren ba.

Zaman lafiya da tsaro tamkar dukiya ce da ya kamata ƙasashen duniya su ririta. A matsayinsu na ƙasashe membobin dindindin a kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya, kana ƙasashe mafiya ƙarfin tattalin arziki na farko da na biyu a duniya, ba kawai raya dangantakar Sin da Amurka bisa hanya madaidaiciya ya kamata mu yi ba, har ma akwai buƙatar mu sauke nauyin dake wuyanmu, don ƙoƙarin taimakawa ga shimfida zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.

Fassarawa: Murtala Zhang