Akwai yiwuwar Liverpool ta lashe Firimiyar bana – Masana

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool ta yi nasara a kan Arsenal da ƙwallaye 2 da nema a wasansu na daren Laraba ƙarƙashin gasar Firimiyar Ingila, wasan da ke da matuƙar muhimmanci ga Liverpool don ganin ta matsa ƙaimi ga Manchester City a tseren da suke na ƙoƙarin lashe kofin gasar.

Har zuwa tafiya hutun rabin lokaci dai babu ƙwallo tsakanin ƙungiyoyin biyu duk kuwa da yadda kowannensu ya riƙa kai farmaki.

A minti na 54 ne Diogo Jota ya zurawa Liverpool ƙwallonta na farko da taimakon Thiago Alcantara gabanin ƙwallon Roberto Firmino wanda ya zura bayan sako shi a fili da taimakaon Andrew Robertson.

Jurgen Klopp dai bai fara wasan na daren Laraba da taurarinsa Mohamed Salah da shi Roberto Firmino sai ana tsaka da wasa ne ya sako su, tare da cire Jota da Diaz a ƙoƙarinsa na rikita lissafin Arsenal wadda ta doka wasan da cikakken karsashi amma ta yi rashin nasara.

Haka zalika, cikin wasanni 18 da vangarorin biyu suka haɗu da juna, sau 1 tal Arsenal ta yi nasara kan Liverpool da ƙwallaye 2 da 1 a watan Yulin 2020, inda galibi ko dai ta yi rashin nasara ko kuma canjaras.

Yanzu haka dai Liverpool ta rage tazarar da ke tsakaninta da Manchester City jagorar gasar zuwa maki 1 tal wanda ke matsayin barazana ga tawagar ta Pep Guardiola wadda a watan jiya ke da tazarar maki 9 a makonnin baya.

Wasan na daren Laraba shi ne haɗuwar ƙungiyoyin biyu karo na 3 a 2022 kuma dukkaninsu Liverpool ke yin nasara ciki har da guda a ƙarƙashin gasar cin kofin ƙalubale da tuni Reds ta lashe kofin bayan doke Chelsea.