Yawan kuɗin ƙetare da aka zuba wa ƙasar Sin a farkon watanni biyu na bana ya ƙaru sosai

CMG HAUSA

Yawan kuɗin ƙetare da suka shigo kasuwar Sin ta ɓangaren da ba na hada-hadar kuɗi ba ya kai RMB Yuan biliyan 243.7, wanda ya ƙaru da kashi 37.9% bisa na makamancin lokaci na bara, inda ya kai matsayin mafi saurin bunƙasuwa tun daga watan Afrilu na shekarar 2021.

Wani manazarci na ganin cewa, saurin shigowar jarin waje a cikin kasuwannin ƙasar Sin ya alamta cewa, Sin ta ci gaba da samun bunƙasuwar tattalin arzikinta, duk da annobar COVID-19 da ta ki ci ta ki cinyewa, da dai sauran matsaloli. Sin na ci gaba da jawo hankali masu zuba jari daga ƙasashen waje.

Kakakin ma’aikatar kasuwancin ƙasar Sin Gao Feng, ya yi tsokaci a taron manema labarai da aka gudanar a jiya Alhamis cewa, yawan jarin da aka samu a farkon watannin biyu na bana ya ƙaru, duk da wasu matsalolin da ake fuskanta. Ya ce:

“Tun daga farkon shekarar bana, tattalin arzikin Sin na samun farfaɗowa sannu a hankali. Ana kuma samun bunƙasuwar buƙatar kayayyaki, inda kasuwar sayayya ke samun farfaɗowa, abin da ya inganta kwarin gwiwar masu zuba jari na waje.

Ƙungiyar kasuwanci ta Amurka da Jamus dake nan ƙasar Sin, ta ba da rahoto a kwanakin baya-bayan nan cewa, kamfanoni masu jarin Amurka da Jamus na da kashi 83% da 96%, sun nuna kyakkyawan fata ga kasuwannin Sin, sa’an nan kamfanonin Amurka na da kashi 66%, kana na Jamus na da kashi 71%, suna kuma shirin kara zuba jari a Sin.”

Fassarawa: Amina Xu