Shugaban ƙaramar Hukumar Dala ya shawarci kansilolin yankin su bai wa cigaban mata da matasa kulawa

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Sabon zaɓaɓɓren Shugaban ƙaramar Hukumar Dala, Alhaji Suraj Ibrahim ya jagoranci rantsar da mataikinsa da sauran zaɓɓaɓɓun kansiloli na yankin a yammacin ranar Lahadi, inda ya umurce su akan su riƙa bijiro da ayyuka da za su amfani cigaban al’umma.

Ya ce su yi aiki tare kuma su bayar da kulawa ta musamman ga bunƙasa ci gaban kamar yadda gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin Abba Kabir ke gudanarwa a jihar.

Alhaji Suraj Ibrahim ya ja hankalin zaɓɓaɓɓun kansiloli da masu riƙe da madafun iko da aka rantsar da su guji yin isgili da zagawa ga waɗanda ba su yi nasara ba.

Ya ce shugabancin ƙaramar hukumar kafin su su zo wasu sun zo kuma sun yi abinda ya kamata mai kyau suma da suka soma yanzu raguwa za su soma yi idan shekaru uku za su yi a wa’adi kwana 360 sau uku kullum kwanaki raguwa suke haka za a tafiya ana ƙirga raguwa ba ƙaruwa ba.

Alhaji Suraj Ibrahim ya ja hankalin sabbin zaɓɓaɓɓun kansilolin na Dala da cewa sune abokan aikinsa kai tsaye sannan ya yi kashedi akan su guji ɗaukar sirrin gwamnati suna fitarwa kamar yadda suka yi alƙawari akai.

Shugaban na ƙaramar hukumar Dala, Alhaji Suraj Ibrahim ya ce za su yi gwamnati na kwatanta adalci domin bunƙasa cigaban al’ummar yankin.

A yayin taron rantsuwar kama aikin an rantsar kansiloli 12 da mataimakin shugaban ƙaramar Hukumar Dala Alhaji Abdul’azeez ɗayyabu Ahmad Meture da sakataren mulki na ƙaramar hukumar Alhaji Sharif Mannir Sharif.

By ukarofi