Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon jagoran ƙungiyar tsagerun Neja Delta, Asari Dokubo, ya bayyana cewa Shugaban ƙasa Bola Tinubu na goyon bayan tsohon gwamnan jihar Ribas kuma ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, don tada hankalin jihar.
Idan za a iya tunawa dai, Wike da gwamna Fubara sun kasance cikin taƙaddama tun bayan da Fubara ya hau kan mulki a matsayin gwamna a shekarar 2023, kamar yadda Fubara ya bayyana cewa rikicinsu da Wike ya samo asali ne daga taƙaddamar iko da sarrafa mulki a jihar Ribas.
Yayin da yake magana a wani shirin talabijin na Arise Tɓ a ranar Talata, Dokubo ya nuna ɓacin ransa kan rikicin da ke gudana a jihar, inda ya ƙara da cewa, “wani abu zai faru” idan aka tsige gwamnan.
“Abin da nake ƙoƙarin faɗa shi ne, da Bola Tinubu ya zama shugaban ƙasa, ya kamata in iya gaya masa gaskiya. Abinda ke faruwa a jihar Ribas inda Bola Tinubu ke goyon bayan Nyesom Wike don tada hankali da tada hankalin jihar Ribas, kuma a matsayina na mai ruwa da tsaki a jihar Ribas, na ji takaicin yadda shugaban ƙasa ya bar ministan dake aiki a ƙarƙashinsa yana yin abinda ya ga dama, yana barazana ga jama’ar jihar Ribas.”