Shugaban Ƙasar Tunusiya Kais Saied, ya kori ministan harkokin addini na ƙasar, bayan da ‘yan ƙasar 49 suka rasa rayukansu a aikin hajjin bana a Ƙasar Saudiyya.
Adadin waɗanda suka mutu ya ƙaru zuwa 1126, fiye da rabinsu daga Masar, kamar yadda kamfanin dillancin labaran AFP ya baya a ranar Juma’a, inda suka haɗa bayanai a hukumance da kuma rahotanni daga jami’an diflomasiyya da ke da hannu a cikin martanin.
“Shugaban ya yanke shawarar kawo ƙarshen ayyukan Ibrahim Chaibi, ministan harkokin addini,” wata sanarwa da fadar shugaban ƙasar ta wallafa a shafin Facebook ta ce ba tare da bayar da wani ƙarin bayani ba.
A ranar Talata ma’aikatar harkokin wajen Tunisia ta ba da rahoton mutuwar mahajjata 35 ‘yan Ƙasar Tunusiya, amma adadin ya ƙaru zuwa 49 a cewar kafafen yaɗa labarai na Tunisiya.
Ma’aikatar ba ta fayyace ko mutuwar na da alaƙa da yanayin zafi ba, inda ta ƙara da cewa galibin waɗanda suka mutu sun tafi Saudiyya ne da bizar yawon buɗe ido, wadda ta saɓa wa dokar shirin gudanar da aikin hajjin na gwamnatin Saudiyya.
Kowacce shekara, ana rarraba izini a hukumance ga ƙasashe ta hanyar tsari kuma ana rarraba wa ɗaiɗaikun mutane ta hanyar caca.
Hakan ya kasance abu mai gudana tun a shekarar 2019 da Saudiyya ta fara bayar da biza ga baƙi masu yawon buɗe ido, wanda hakan ya kawo sauƙin balaguro zuwa yankin Gulf.
Ƙasashen Malaysia, Indiya, Jordan, Iran, Senegal, Tunisia, Sudan da kuma yankin Kurdistan mai cin gashin kansa na Iraki sun tabbatar da mutuwar a lokacin aikin hajji.
