Shugaban Ghana da ministocinsa sun zabtare albashinsu da kashi 30 don rage kashe kuɗaɗen gwamnati

Shugaban ƙasar Ghana, Nana Akufo-Addo tare da ministocinsa sun zabtare albashinsu da kashi 30 don rage kashe kuɗin gwmanati a daidai lokacin da ƙasar ke ci gaba da fama da tsadar man fetur sakamakon yaƙin Ukraine wanda ya yi tasiri a kan ƙasar kamar yadda gwamnatin ƙasar ta bayyana a jiya Alhamis.

Ministan kuɗi na ƙasar, Ken Ofori-Atta ya bayyana cewa, daga yanzu an dakatar da tafiye-tafiyen jami’an gwamnati zuwa ƙetare sai in dan wani alma’ari mai matuƙar muhimmancin gaske, haka ma an dakatar da sayo motoci daga waje, tare da cewa wannan mataki ya soma aiki ne nan take.

Ministan ya ci gaba da cewa, gwamnati na sa ran taƙaita kashe kuɗaɗe da kusan Dala miliyan 400 albarkacin wannan mataki da ta ɗauka.

A halin yanzu dai yaƙin da ake gwabzawa tsakanin Rasha da Ukraine ya yi sanadiyar tashin farashin mai a faɗin duniya wanda haka ya haifar da tsadar rayuwa da ya shafi ƙasashen Afirka ta Yamma.

Kazalika, ya ce gwmanatin Ghana na ƙoƙarin ganin ta yauƙaƙa harajin da take tarawa a cikin gida don ƙara yawan kuɗaɗen shigar da take samu.