Shugaban IOC ya yaba da fasahar CMG

Daga CRI HAUSA

Ranar 18 ga wata, shugaban kwamitin wasan Olympic na ƙasa da ƙasa wato IOC ya shirya taron manema labaru, inda shugaban kwamitin Thomas Bach ya ce, yayin da ake gudanar da gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing, an gwada fasahohi iri daban-daban, musamman ma mabambantan fasahohin zamani mallakar babban gidan rediyo da talibijin na ƙasar Sin na CMG, waɗanda suka ba shi mamaki sosai. Ya yi imanin cewa, fasahohin ƙasar Sin za su ƙara ba da gudummawa kan wasannin Olympics a nan gaba.

Shugaban IOC ya ƙara da cewa, an samu nasara sosai a gasar ta Beijing, inda ‘yan wasa suka ji daɗi sosai, sun kuma gamsu sosai kan filayen wasa, kauyen Olympic, hidimomi masu ruwa da tsaki da ma yadda ake yaqi da annobar COVID-19.

Fassarawa: Tasallah Yuan